Kungiyar tabbatar da adalci da daidaito kan Tattalin arziki ta SERAP ta shigar da karat gwamnatin shugaban kasa Tinubu kan abinda ta ce rashin adalci da sabawa doka kan karin kaso 50 na kudin sadarwar da hukumar sadarwa ta kasar NCC ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi.
A baya bayan nan ne dai hukumar sadarwa ta NCC ta amince da karin kaso 50 cikin 100 na kudaden sadarwa na kira da na data a fadin kasar.
A karar da ta shigar a ranar Juma’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman kotun da ta yi duba kan hukuncin da hukumar NCC ta yanke na baiwa kamfanonin sadarwa damar karin kaso 50 cikin dari na sadarwa,abinda ta kira rashin adalci tare da take hakkin ‘yan kasar
Sabon karin an yi kiyasin farashin kira zai tashi zuwa naira 16, a duk minti guda, farashin data 1GB, zai tashi zuwa naira 431 ya yinda farashin tura sako zai koma naira 6 daga naira 4.
