Kamfanin safarar mutane ta manhajar Bolt ya samu karuwar sabbin rijistar direbobi da kashi 92 cikin 100 a Najeriya cikin mako guda, bayan ficewar babban abokin hamayyarsa, Uber, daga kasuwar kasar.
Bolt, wanda kamfanin fasahar zirga-zirga ne daga Estonia, ya bayyana cewa karuwar rijistar ta biyo bayan ficewar Uber daga Najeriya, yayin da direbobi ke neman wasu hanyoyin ci gaba da samun kudaden shiga.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya aika wa PUNCH Online ranar Laraba.
Uber ta dakatar da ayyukanta a Najeriya a ranar 2 ga Satumba, bayan shafe kusan shekaru 12 tana aiki a kasar. Ficewar kamfanin ta sa wasu direbobi da fasinjoji ke neman wasu manhajojin safarar mutane a cikin yanayin da ake fama da hauhawar kudin man fetur, gyaran motoci da sauran kudaden gudanar da harkokin sufuri.
Babban Manajan Bolt na Yammacin Afirka, Teddy Appa-Dankyi, ya ce kamfanin ya samu karin kashi 92 cikin 100 na rijistar direbobi daga mako zuwa mako bayan ficewar Uber.
Sai dai Bolt bai bayyana adadin direbobin da suka yi rijista kafin da kuma bayan ficewar Uber ba, don haka ba a san ainihin yawan direbobin da wannan karin kashi 92 cikin 100 ya kunsa ba.
Appa-Dankyi ya ce duk da karuwar masu neman shiga Bolt, kamfanin ba zai sassauta ka’idojin tantance direbobi da matakan tsaro ba.
Ya ce duk direban da ke son shiga Bolt dole ne ya bi matakan tantancewa da ka’idojin tsaro da kamfanin ya tanada.
Haka kuma, kamfanin ya ce direbobin da aka dakatar ko aka toshe daga amfani da manhajar saboda manyan laifukan da suka shafi tsaro, rashin da’a ko karya ka’idoji ba za su samu damar komawa cikin manhajar kai tsaye ba.
A cewar Bolt, karuwar masu neman zama direbobinsa na nuna yadda direbobi ke neman wasu hanyoyin ci gaba da aiki bayan ficewar Uber daga Najeriya.
Kamfanin ya ce zai ci gaba da zuba jari wajen bunkasa manhajarsa da kuma tallafa wa al’ummar direbobinsa yayin da kasuwar safarar mutane ta manhajoji ke ci gaba da sauyawa a Najeriya.
