Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-Ƙirƙire, Hannatu Musawa, ta bayyana alhininta kan rasuwar fitaccen jarumin Nollywood, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs, yana da shekaru 84.
Ministar ta bayyana rasuwar jarumin a matsayin babban rashi ga Najeriya da masana’antar nishaɗi, tana mai cewa gudunmawar Olu Jacobs ga harkokin fasaha ta shafe sama da shekaru 50.
A cikin wata sanarwa da mai ba ta shawara kan harkokin yaɗa labarai, Nneka Anibeze, ta fitar a Abuja ranar Laraba, Musawa ta bayyana Olu Jacobs a matsayin “cibiyar ƙasa” kuma ɗaya daga cikin ginshiƙan masana’antar nishaɗin Najeriya.
Ta ce Olu Jacobs ba ɗan wasan kwaikwayo kawai ba ne, domin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman Afirka, wanda muryarsa, kwarewarsa da kasancewarsa a fagen wasan kwaikwayo suka taimaka wajen ba da muhimmanci ga labaran Najeriya da kuma haɓaka martabar masana’antar.
Musawa ta kuma yaba da gudunmawar da Olu Jacobs ya bayar wajen horas da sabbin masu fasaha ta hanyar Lufodo Academy, wadda ya kafa tare da matarsa kuma fitacciyar jaruma, Joke Silva.
A cewar ministar, makarantar ta horas da daruruwan ’yan wasan kwaikwayo, daraktoci da masu shirya fina-finai, waɗanda daga baya suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Nollywood.
Ta ce gadon da Olu Jacobs ya bari zai ci gaba da rayuwa a fagen wasan kwaikwayo, fina-finai da zukatan miliyoyin ’yan Najeriya da suka yi shekaru suna kallon ayyukansa.
“Nigeria has lost a Lion, but his light will never fade,” in ji Musawa.
Olu Jacobs na daga cikin fitattun mutane da suka taka rawa wajen bunƙasa harkokin wasan kwaikwayo, talabijin da fina-finai a Najeriya. Ayyukansa sun shafe shekaru da dama, ciki har da fitowarsa a wasu shirye-shiryen talabijin da fina-finai a Najeriya da ƙasashen waje.
Ya yi karatu a Royal Academy of Dramatic Art da ke Landan, kafin ya fara samun karɓuwa a fagen wasan kwaikwayo da talabijin a Birtaniya, sannan daga baya ya koma Najeriya inda ya zama ɗaya daga cikin manyan fuskokin Nollywood.
Baya ga wasan kwaikwayo, Olu Jacobs da Joke Silva sun kafa Lufodo Group, wadda ke da alaka da harkokin shirya fina-finai da kuma ilimin fasahar wasan kwaikwayo.
Gudunmawarsa ga masana’antar fasaha ta sa Gwamnatin Tarayya ta karrama shi da lambar girma ta ƙasa ta Member of the Order of the Federal Republic (MFR).
Ministar ta miƙa ta’aziyyarta ga Joke Silva, ’ya’yansu, sauran ’yan uwa da abokan arziki, da kuma miliyoyin ’yan Najeriya da suka yi kaunar ayyukan fitaccen jarumin.
Rasuwar Olu Jacobs ta kawo ƙarshen rayuwar ɗaya daga cikin manyan jaruman da suka taimaka wajen kafa tarihi da kuma samar da makoma ga masana’antar fina-finan Najeriya.
