Fitattun jaruman Nollywood da mawakan Fuji sun shiga cikin jerin fitattun ’yan masana’antar nishaɗi da aka nada a kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC ta Jihar Legas.
Daga cikin wadanda aka bayyana sunayensu akwai tsohon jarumi Jide Kosoko, da mawakan Fuji Wasiu Alabi Pasuma, Abass Akande Obesere da Adewale Ayuba, tare da jaruman Nollywood Toyin Abraham, Eniola Badmus da Bimbo Akintola.
An bayyana cikakken tsarin kwamitin ne a ranar Alhamis ta hannun Kadri Obafemi Hamzat Media Centre, gabanin bikin rantsar da kwamitin da aka shirya gudanarwa ranar Juma’a, 18 ga Satumba, a sakatariyar APC da ke ACME Road, Ikeja.
A cikin sashen Entertainment and Creative Economy Directorate, Toke Benson-Awoyinka ce za ta jagoranci matsayin Darakta, yayin da Jide Kosoko zai kasance Co-Director, Eniola Badmus kuma Deputy Director.
Akeem Alimi, wanda aka fi sani da Ajala Jalingo, an sanya shi a matsayin Sakataren sashen, yayin da Dare Olateju zai kasance Mataimakin Sakataren.
Haka kuma, jerin sunayen ya kunshi wasu fitattun ’yan wasan kwaikwayo na masana’antar fina-finan Yarbanci, ciki har da Oga Bello (Adebayo Salami), Saheed Balogun, Bukky Wright, Fathia Balogun, Yinka Quadri da Tayo Sobola.
Bangaren mawakan Fuji ma ya samu wakilci sosai, inda aka hada da Pasuma, Obesere, Adewale Ayuba, Sulaimon Alao Adekunle wanda aka fi sani da Malaika, Akorede Babatunde Okunola (Osupa), da Temitope Adekunle (Small Doctor).
Sashen Entertainment and Creative Economy Directorate na daga cikin bangarorin da aka kafa karkashin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na Jihar Legas.
A tsarin shugabancin kwamitin, an bayyana Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a matsayin Shugaba, yayin da Kadri Obafemi Hamzat zai kasance Mataimakin Shugaba.
Shigar fitattun jarumai da mawakan Fuji cikin kwamitin na kara nuna yadda jam’iyyar ke hada masu ruwa da tsaki a masana’antar nishaɗi da harkokin kirkire-kirkire cikin tsarin yakin neman zabenta na jihar.
