Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bai wa masu aikata laifuka da ke amfani da dazuzzukan jihar a matsayin mafaka wa’adin kwanaki 14 su fice daga cikinsu.
Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan kan Harkokin Gandun Daji, Bidemi Obayangban, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Akure ranar Laraba.
Obayangban ya ce umarnin gwamnan ya fi mayar da hankali kan masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka da ke fakewa a cikin dazuzzukan jihar domin gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar na inganta tsaro da kuma samar da yanayin da zai ba manoma, masu zuba jari da sauran masu gudanar da harkokin kasuwanci damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
A cewarsa, tsaro na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da nasarar shirin gwamnatin jihar na bunkasa fannin gandun daji da kuma jawo masu zuba jari.
Obayangban ya ce jami’an tsaro da mafarauta a fadin jihar suna aiki tare da gwamnati wajen dakile garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a dazuzzukan.
Ya ce gwamnatin Aiyedatiwa ta kammala shirye-shiryen da za su taimaka wajen “kwashe” masu aikata laifuka daga dazuzzukan jihar, tare da mayar da su wuraren da za a iya gudanar da ayyukan tattalin arziki na halal.
“Gwamnatin jihar tana ba wadannan mutane kwanaki 14 su bar dazuzzukan Ondo. Idan suka ki, za su fuskanci sakamakon abin da suka aikata,” in ji Obayangban.
Ya kara da cewa dawo da tsaro a dazuzzukan na da matukar muhimmanci wajen farfado da harkokin gandun daji, da kuma tabbatar da cewa manoma, masu zuba jari da ’yan kwangilar katako za su iya gudanar da ayyukansu ba tare da fargabar hare-haren masu laifi ba.
Gwamnatin jihar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da aiki da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin dawo da cikakken tsaro a dazuzzukan Ondo.
