Hukumar Kula da Tattalin Arzikin Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPERA) ta bayyana cewa samar da ingantattun tashoshin jiragen ruwa masu gasa na da matukar muhimmanci wajen cimma burin Gwamnatin Tarayya na gina tattalin arzikin Najeriya da zai kai darajar dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030.
Darakta-Janar na NPERA, Dakta Pius Akutah, ne ya bayyana hakan a Legas yayin da Shugaban Kungiyar Masu Rahoto kan Harkokin Jiragen Ruwa ta Najeriya (SCAN), Moses Ebosele, ya jagoranci wata tawaga zuwa ziyarar ban girma a hukumar.
Akutah ya ce NPERA ta mayar da hankali wajen sauya tsarin kula da tashoshin jiragen ruwa ta hanyar karfafa dokoki, samar da ka’idoji, amfani da fasahar zamani da kuma mayar da harkokin aiki zuwa tsarin zamani na dijital.
Ya bayyana cewa hukumar ba ta da alhakin tsara harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwa kawai, har ma tana da ikon tabbatar da bin ka’idoji da hukunta ayyukan da ka iya kawo cikas ga kasuwanci da ingancin ayyukan tashoshin ruwa.
A cewarsa, sabuwar dokar NPERA ta bai wa hukumar karfin daukar mataki kan wadanda suka karya ka’idoji, sabanin tsarin da ya gabata karkashin Hukumar Kula da Masu Safarar Kaya ta Najeriya.
Akutah ya ce mafi karancin hukuncin kudi ga mutum da ya aikata laifi a karon farko ya kai N500,000, yayin da kamfani zai iya fuskantar tarar da ta kai N20m. Ya kuma ce hukuncin na iya karuwa idan aka ci gaba da maimaita karya doka.
Duk da haka, ya jaddada cewa manufar hukumar ba ita ce kawo tsaiko ko rikita harkokin tashoshin ruwa ba, sai dai samar da tsarin da zai sa masu ruwa da tsaki su bi ka’idojin da aka shimfida.
Ya kuma bayyana cewa kara amfani da na’urorin zamani da rage shiga tsakani na mutane a harkokin tashoshin jiragen ruwa zai taimaka wajen rage tsaiko, saukaka fitar da kaya da kuma rage kudaden da ake kashewa wajen gudanar da harkokin kasuwanci.
Game da korafe-korafen cewa hukumomin gwamnati da dama na gudanar da bincike a tashoshin ruwa, Akutah ya ce NPERA ba ta da niyyar hana sauran hukumomin gwamnati gudanar da ayyukan da doka ta ba su. Sai dai ya bukaci a gudanar da irin wadannan bincike cikin tsari ba tare da jinkirta fitar da kaya daga tashoshin ruwa ba.
Akutah ya danganta ingancin tashoshin ruwa da burin Najeriya na gina tattalin arzikin da zai kai dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030. Ya ce bai kamata a mayar da hankali kawai kan kudaden shiga da gwamnati za ta samu ba, domin bunkasar tattalin arziki ta hada da karuwar kasuwanci da ayyukan kamfanoni da ’yan kasuwa.
Ya kuma bayyana cewa babu rikici tsakanin NPERA da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), domin kowacce hukuma tana da nata nauyin da doka ta dora mata. A cewarsa, NPA ce ke da alhakin bunkasa ababen more rayuwa na tashoshin ruwa, yayin da NPERA ke kula da tsarin tattalin arziki da dokokin gudanar da tashoshin.
A nasa bangaren, Shugaban SCAN, Moses Ebosele, ya taya shugabanci da ma’aikatan NPERA murnar sabon nauyin da aka dora wa hukumar. Ya ce ingantaccen tsari da kuma kyakkyawar sadarwa tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki za su taimaka wajen bunkasa harkokin sufurin ruwa da saukaka kasuwanci a Najeriya.
Ebosele ya kuma gayyaci Darakta-Janar na NPERA zuwa taron SCAN na shekarar 2026, wanda aka shirya gudanarwa a Legas ranar 29 ga Oktoba, 2026.
