Kamfanin ƙididdigar bashi na DataPro ya bayyana cewa sabuwar Hukumar Ƙididdigar Bashi ta Afrika (AfCRA) za ta samu karɓuwa a kasuwannin kuɗaɗen nahiyar ne kawai idan ta kasance mai zaman kanta, mai gaskiya da kuma bin ƙa’idojin ƙwararru wajen gudanar da aikinta.
A cikin rahotonsa na watan Agusta, DataPro ya ce ingantacciyar hukumar ƙididdigar bashi dole ne ta kasance mai cin gashin kanta, mai bayyana hanyoyin tantancewa a fili, mai zurfin bincike, mai kyakkyawan tsarin gudanarwa da kuma bayar da hujjojin da ke bayyana dalilan da suka sa aka bayar da kowace ƙima.
Kamfanin ya ce yayin da AfCRA ke faɗaɗa ayyukanta, masu ruwa da tsaki na sa ran za ta tabbatar da cewa dukkan matakan tantancewa suna gudana cikin tsari ɗaya kuma ana bayyana su ga jama’a.
A cewar DataPro, bayyana cikakkun dalilan ƙididdiga, hasashen da aka yi amfani da shi da kuma ƙa’idojin bincike zai ƙara wa masu zuba jari kwarin gwiwa kan sahihancin sakamakon ƙididdigar.
Rahoton ya jaddada cewa martabar kowace hukumar ƙididdigar bashi ba ta ginuwa cikin dare ba, sai da lokaci da kuma kyakkyawan tarihi na gudanar da aiki.
Ya bayyana cewa yayin da AfCRA ke fara tantance gwamnatoci, kamfanoni da cibiyoyin kuɗi, masu zuba jari za su duba yadda ƙididdigarta ke kasancewa mai daidaito, saurin ɗaukar mataki idan akwai sauye-sauye, da kuma yadda ƙididdigar ke dacewa da abin da ya faru daga baya.
DataPro ya kuma ce domin samun amincewa na dogon lokaci, AfCRA dole ne ta tabbatar da ‘yancin kai daga tasirin siyasa da na kasuwanci, bin ƙa’idoji masu bayyana a fili, ingantaccen tsarin gudanarwa da kuma bayar da ƙididdigar da ke nuna ainihin haɗarin bashi.
Kamfanin ya ƙara da cewa yayin da buƙatar kuɗaɗen ci gaba ke ƙaruwa a Afrika, tare da bunƙasar kasuwannin takardun bashi na cikin gida, samun ingantacciyar hukumar ƙididdigar bashi ta nahiyar zai taimaka wajen rage dogaro da hukumomin ƙasashen waje, samar da ƙididdigar da ta dace da yanayin Afrika da kuma rage tsadar samun jari ga gwamnatoci da kamfanonin nahiyar.
