Gwamnatin Jihar Legas ta horas da ma’aikata 400 na Unified Local Government Service domin taimaka musu su yi shiri yadda ya kamata kafin yin ritaya daga aikin gwamnati.
An gudanar da horon ne a ƙarƙashin Taron Wayar da Kai na Masu Shirin Yin Ritaya na 2026, wanda Ofishin Local Government Establishments and Training ya shirya a Adeyemi-Bero Auditorium da ke Alausa, Ikeja.
Da take jawabi a wajen taron, Babbar Sakatariya ta ofishin, Toyin Ogunlana, ta bayyana cewa bai kamata a ɗauki ritaya a matsayin ƙarshen rayuwar aiki ba, sai dai a matsayin farkon wani sabon babi da ke buƙatar kyakkyawan shiri.
Ta ce an shirya taron ne domin bai wa ma’aikatan da ke dab da ritaya ilimi da ƙwarewar da za su taimaka musu wajen yanke shawara mai kyau bayan sun bar aiki.
A cewarta, ma’aikata da dama na fuskantar matsaloli bayan ritaya saboda rashin isasshen sani kan tsarin fansho, yadda ake tsara harkokin kuɗi, kula da lafiya da kuma hanyoyin ci gaba da gudanar da rayuwa cikin amfani.
Ogunlana ta ƙara da cewa mutane da dama kan fara tunanin ritaya ne a shekarun ƙarshe na aikinsu, lamarin da kan jawo rashin shiri.
Ta bayyana cewa taken taron na bana, “Retirement Ready: Ensuring a Seamless Transition from Service to Pension,” ya mayar da hankali ne kan muhimmancin fara shirin ritaya da wuri, fahimtar tsarin fansho da kuma samar da ingantaccen tsari na rayuwa bayan aiki.
A nasa saƙon fatan alheri, Darakta Janar na Hukumar Fansho ta Jihar Legas (LASPEC), Babalola Obilana, ya yaba da ci gaba da shirya irin wannan taro duk shekara.
Ya buƙaci ma’aikatan da ke shirin yin ritaya su tabbatar bayanansu na fansho sun kasance daidai, tare da ci gaba da tuntuɓar Pension Fund Administrators (PFAs) domin kauce wa jinkiri wajen karɓar haƙƙoƙinsu.
Ita ma Babbar Sakatariya ta Local Government Service Commission, Bukonla Durodola, ta ƙarfafa gwiwar mahalarta taron da su kalli ritaya a matsayin wata sabuwar dama ta ci gaba da rayuwa mai amfani, tare da yin shiri tun kafin lokacin ya yi.
