Wata jinyar lafiya a kasar Thailand ta karya wata al’adar addinin Buddha da ke hana mata taba sufaye domin ceton rayukansu bayan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar sufaye 10.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a lardin Mukdahan da ke arewa maso gabashin Thailand, lokacin da wani yaro mai shekara 11 ya dauki motar iyayensa ba tare da izininsu ba, inda ya kutsa cikin jerin gwanon sufaye 35 da wasu mabiya addinin guda biyar.
Mintuna kadan bayan hatsarin, jinyar mai suna Wiwat Laonoi ta isa wurin tare da fara ba da agajin gaggawa, duk da gargadin wasu cewa bai dace mace ta taba su ba saboda al’adar addinin Buddha.
Ta ce, “Wasu sun ce mini, ‘Dakata, sufaye ne!’, amma na ce a wannan lokacin ba sufaye ba ne, marasa lafiya ne da ke bukatar ceto.”
Wiwat, wadda ta shafe kusan shekaru 40 tana aikin jinya, ta ce ita ce mutum ta farko da ta isa wurin hatsarin, kuma ba ta taba ganin irin wannan mummunan lamari ba a rayuwarta.
Ta bayyana cewa nan take ta fara duba bugun zuciyar wadanda suka jikkata, ta yi wa wasu aikin farfado da numfashi (CPR), sannan ta hada kai da asibitin yankin domin kai dauki cikin gaggawa.
Mutane biyar daga cikin sufayen sun mutu nan take a wurin hatsarin, yayin da wasu biyar suka rasu daga baya a asibiti. Har zuwa ranar Juma’a, wasu mutum 10 na ci gaba da karbar magani a asibiti, ciki har da biyu da ke cikin mawuyacin hali.
Wata ma’aikaciyar asibiti mai suna Parichat Kochakueng, wadda ke tare da Wiwat lokacin da hatsarin ya faru, ta ce abin ya kasance mai matukar tayar da hankali, domin ta ga sufaye da dama kwance a kan hanya.
Wiwat, wadda ta fito daga lardin Mukdahan, ta ce tana fatan ci gaba da aikin sa kai wajen ba da kulawar lafiya a yankunan da ke fama da karancin ma’aikatan lafiya bayan ta yi ritaya a watan Satumba.
Ta ce tana alfahari da samun damar amfani da iliminta wajen ceton rayukan jama’a ba tare da la’akari da bambancin addini ko al’ada ba.
