Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) sun kama tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a filin jirgin sama na Akanu Ibiam International Airport da ke Enugu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama Nnaji ne da safiyar Laraba yayin da yake shirin hawa wani jirgi mai zaman kansa zuwa Abuja.
A cewar majiyoyin, DSS ta aiwatar da kamen ne bisa buƙatar Hukumar ICPC, wadda ke gudanar da bincike kan wasu zarge-zargen da ake yi wa tsohon ministan.
Bayan kama shi, an miƙa Nnaji ga jami’an ICPC domin ci gaba da gudanar da bincike.
Wata majiya ta ce, ICPC ta sha aika masa da gayyata domin amsa tambayoyi kan wasu koke-koke da suka shafi yadda aka gudanar da harkokin Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha a lokacin da yake minista.
Sai dai, bayan ya kasa amsa gayyatar da aka yi masa sau da dama, hukumar ta nemi taimakon DSS domin kama shi.
An tuna cewa Uche Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa na Ministan Kimiyya da Fasaha a watan Oktoban shekarar da ta gabata, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, DSS da ICPC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan kamen ba, yayin da Uche Nnaji ma bai yi wata magana kan zarge-zargen da ake yi masa ba.
Haka kuma, ƙoƙarin samun martani daga kakakin ICPC, John Odeh, bai yi nasara ba kafin wallafa wannan rahoto.
