Kamfanin Guinness Nigeria Plc ya yi kira ga hukumomi, kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki da su kara hada kai wajen yaki da jabun kaya, musamman a wannan zamani na fasahar kirkirar basira (AI) da kasuwancin intanet.
Babban Darakta kuma Shugaban Kamfanin Guinness Nigeria, Girish Sharma, ya bayyana hakan yayin wani taro da kamfanin ya shirya tare da kungiyar Anti-Counterfeiting Collaboration of Nigeria (ACC) a Legas domin bikin Ranar Yaki Da Jabun Kaya ta Duniya ta 2026.
Taron ya hada shugabannin masana’antu, hukumomin gwamnati, jami’an tsaro da masu mallakar tambura domin tattauna yadda ake samun karuwar jabun kaya a duniya da hanyoyin magance matsalar.
Da yake wakiltar Sharma, Daraktan Hulda da Jama’a da Harkokin Shari’a na Guinness Nigeria, Rotimi Odusola, ya ce masu jabun kaya na amfani da shafukan kasuwanci na intanet, kafafen sada zumunta da kuma sabbin fasahohin AI wajen kera da tallata kayayyakinsu cikin sauki.
“Jabun kaya ba ya takaita ga kasuwanni na gargajiya kawai. Yanzu ya zama wata babbar matsala ta kasa da kasa da ke anfani da fasahar zamani wajen yada kayayyakin bogi,” in ji shi.
Ya kara da cewa duk da cewa fasahar zamani ta samar da karin dama ga masu jabun kaya, ita ma tana ba da hanyoyi masu inganci wajen gano laifuffuka, musayar bayanan sirri da kuma dakile ayyukan masu aikata wannan laifi.
Shugaban kungiyar ACC, Sola Dosumu, wanda ya jagoranci taron, ya jaddada bukatar kara hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin dakile matsalar.
A nata bangaren, Daraktar Ayyuka ta Hukumar SON a Legas, Tessy Ojomo, ta ce tsaurara hukunci da tabbatar da bin ka’idojin tantance kayayyaki na taimakawa wajen rage yaduwar jabun kaya.
Haka kuma, Daraktan Bincike da Aiwatar da Doka na NAFDAC, Dakta Martins Iluyomade, ya bukaci masu kamfanoni su kare tamburansu tare da daukar matakan dakile masu jabun kaya.
Sharma ya jaddada cewa fasaha kadai ba za ta iya magance matsalar ba, yana mai cewa akwai bukatar cikakken hadin kai tsakanin kamfanoni, gwamnati, jami’an tsaro da masu samar da fasaha domin samun nasara.
Ya ce, “Idan muka hada kai, za mu iya anfani da AI da fasahar zamani wajen kasancewa gaba da masu jabun kaya da kuma kare masu amfani da kayayyaki.”
Taron ya samu halartar wakilan Hukumar Kwastam ta Najeriya, FCCPC, ACC da shugabannin Guinness Nigeria, inda aka kammala da alkawarin kara karfafa hadin gwiwa wajen yaki da jabun kaya da kare masu amfani da kayayyaki.
