Dan wasan gaba na Faransa, Ousmane Dembélé, ya bayyana Lionel Messi a matsayin mafi kyawun dan kwallon kafa da ya taba gani a rayuwarsa, yana mai yabawa hazakar tauraron dan wasan Argentina duk da shekarunsa.
Dembélé ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Marca, inda ya ce Messi har yanzu yana taka rawar gani a matakin koli duk da cewa yana daf da kaiwa karshen rayuwarsa ta kwallon kafa.
“Lionel Messi shi ne mafi kyawun dan wasa da na taba gani. Yana da shekara 38 amma har yanzu yana da matukar kwarewa kuma yana da hadari ga kowace kungiya. Hazakarsa ba ta tsufa,” in ji Dembélé.
Tauraron dan wasan na Paris Saint-Germain (PSG), wanda ya taba taka leda tare da Messi a Barcelona da kuma PSG, ya gargadi masu adawa da kada su raina fitaccen dan wasan.
Ya ce, “Dole ne kowa ya yi hattara. Leo Messi har yanzu yana iya lashe Kofin Duniya.”
Messi, wanda ya jagoranci Argentina zuwa lashe Kofin Duniya na 2022 a Qatar, na ci gaba da taka leda a babban mataki kuma har yanzu yana daga cikin manyan taurarin kwallon kafa a duniya.
Masana da magoya baya da dama na kallon Messi a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan wasa mafiya tasiri a tarihin kwallon kafa, kuma har yanzu yana da damar canja akalar manyan gasa a duk lokacin da ya taka fili.
Kalaman Dembélé sun sake nuna irin girmamawa da darajar da Messi ke da ita a idon abokan wasansa da kuma duniyar kwallon kafa baki daya.
