‘Yar wasan mai shekaru 33, wadda ta taba wakiltar Birtaniya a gasar Olympics, ta kammala tseren cikin sa’o’i 2 da mintuna 43.
Ko da yake wannan lokaci bai kai mafi kyawunta ba, amma ana kallon nasarar a matsayin abin ban mamaki duba da halin da take ciki.
“Ina godiya da na iya kammala wannan tseren. Mil 26.2 ba abu bane mai sauki, balle kuma ina dauke da ciki,” in ji ta.
KALUBALEN DA TA FUSKANTA
A farkon tseren, Hauger-Thackery ta fuskanci matsala mai tsanani bayan wata jijiyar jiki ta makale a bangaren kugu (glute), wanda hakan ya hana ta tafiya yadda ya kamata.
“Ban ma iya daga kafata ta dama yadda ya kamata ba, sai ja nake yi,” in ji ta.
Ta kuma shiga dakin jinya domin samun kulawa, sannan ta sake samun taimako a mil na 11 kafin ta ci gaba da tseren.
TASIRIN CIKI
Saboda dauke da ciki, ta bayyana cewa dole ta rika tsayawa lokaci-lokaci, musamman kafin kaiwa rabin tseren.
“Na tsaya sau biyu saboda fitsari, kamar yadda yake ga masu ciki,” ta bayyana.
SAUYA HALI A RABIN NA BIYU
Duk da wahalhalun da ta fuskanta a farko, rabin na biyu na tseren ya kasance cikin sauki gare ta.
“Na ji jikina ya daidaita sosai, kamar komai ya dawo daidai. Amma kafin rabin tseren, ban ma yi tunanin zan kammala ba,” in ji ta.
