Duchess of Sussex, Meghan Markle, ta fito a matsayin bakuwar alkali a shahararren shirin dafa abinci na Australia, MasterChef Australia, inda ta taimaka wajen jagorantar wasu daga cikin masu dafa abinci na gida.
Rahotanni sun nuna cewa Meghan ta halarci shirin ne yayin ziyarar da ta kai Australia tare da mijinta, Prince Harry, wanda ya gudanar da wasu ayyuka daban a ranar 15 ga Afrilu, ciki har da ziyara zuwa ƙungiyar Movember da kuma ganawa da tsoffin sojoji a Canberra War Memorial.
A cikin shirin, an ce Meghan ta bayar da shawarwari da jagoranci ga mahalarta gasar tare da sauran alkalai kamar Poh Ling Yeow, Sofia Levin da Jean-Christophe Novelli.
Wani bidiyo da tashar Channel 10 ta Australia ta wallafa a Instagram ya nuna yadda aka gabatar da Meghan ga mahalarta shirin, inda suka yi tafi da murna.
Poh Ling Yeow ta ce:
“Mun taɓa samun manyan jarumai a MasterChef, amma babu kamar wannan.”
Haka kuma shafin MasterChef Australia ya bayyana a Instagram cewa Meghan ta kasance “ta musamman” a cikin shirin, tare da tabbatar da dawowarta Australia a karon farko tun 2018.
An bayyana cewa za ta kasance cikin jerin fitattun baƙi da masana abinci da ke fitowa a shirin wannan kakar.
