Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Belgium, Club Brugge, na daga cikin manyan kungiyoyin da ke zawarcin matashin dan wasan Najeriya, Zadok Yohanna, bisa ga rahoton voetbalnieuws.
Dan wasan mai shekaru 18, wanda ke taka leda a kungiyar Sweden ta AIK, ya fara jan hankali sosai sakamakon bajintarsa a kakar wasa ta bana, inda ya zura kwallaye 4 tare da taimakawa aka zura 2 a wasanni 12 kacal.
Rahotanni sun bayyana cewa Club Brugge ba ita kadai ba ce ke bibiyar sa, domin manyan kungiyoyin Turai kamar Ajax da Chelsea suma suna cikin jerin kungiyoyin da ke sha’awar sa.
Yohanna, wanda kwantiraginsa da AIK zai kare a ranar 31 ga Disamba 2029, na nufin cewa duk wata kungiya da ke son sa dole ne ta gabatar da tayin da zai gamsar da kulob dinsa na Sweden.
A baya-bayan nan, ‘yan wasa matasa daga gasar Sweden sun rika tafi Turai kan kuɗi mai yawa, wanda ya kai tsakanin Euro miliyan 9 zuwa 20, lamarin da ke nuna cewa Yohanna zai iya zama mai tsada a kasuwa.
An haifi Yohanna ne a Bauchi, Najeriya, inda ya fara harkar kwallon kafa a Ikon Allah Football Academy kafin daga bisani AIK ta dauke shi a shekarar 2025.
Tun bayan komawarsa Sweden, ya samu saurin shiga cikin kungiyar farko, inda ya fara taka leda a kakar 2026.
An bayyana shi a matsayin dan wasa mai fasaha, sauri mai tsanani, da kuma iya kirkirar dama a gaba. Shi dan hagu ne amma yana taka leda a gefen dama, kuma yana iya taka rawar attacking midfield idan bukata ta taso.
Yayin da ake ci gaba da bibiyar sa a kasuwar ‘yan wasa ta Turai, ana ganin Yohanna na daga cikin matasan ‘yan wasan Najeriya masu haske da za su iya kaiwa matakin koli a n an gaba.
