Fitaccen ɗan wasan barkwanci na Najeriya, I Go Save, ya mayar da martani kan rahotannin rikicin auren tsohuwar jarumar shirin Big Brother Naija, Angel Smith.
Rahotanni sun bayyana cewa Angel Smith, wadda ta yi aure da abokiyar zamanta Tumininu makonni kaɗan da suka gabata, yanzu tana cikin rikici bayan zargin da ake yi mata na cin amana a cikin auren.
A cewar rahoton, Tumininu ta zargi Angel da alaƙa da wata mace da ta hadu da ita ta hanyar manhajar Hinge, lamarin da ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Tumininu ta kuma bayyana cewa ta kashe kuɗi mai yawa a kan Angel tun zuwanta Amurka, ciki har da sama da dala $100,000 da kuma kusan $50,000 a ranar haihuwarta, kafin rikicin ya fara bayyana.
A martanin da ya wallafa a shafinsa na Instagram, I Go Save ya bayyana cewa:
“Men are really trying when it comes to marriage matters.
A woman got married to a woman, and the marriage didn’t even last 70 hours.
She couldn’t handle what the other woman was doing.”
Wannan batu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke ta mayar da martani kan yadda lamarin ya faru cikin gaggawa bayan aure.
Rikicin na ci gaba da jan hankalin jama’a, yayin da bangarorin biyu har yanzu ba su fito da cikakken bayani na hukuma ba kan halin da ake ciki.
