Kungiyar Malaman Najeriya, NUT, ta nuna damuwarta kan rashin aiwatar da sabon tsarin albashi na musamman ga malaman makarantun firamare da sakandare, wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Mataimakin Shugaban NUT na Ƙasa, Kizito Kalu, ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin, yayin gabatar da jawabin kungiyar na bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2026 da aka gudanar a Eagle Square.
Taken bikin na bana shi ne “Standing with teachers: 60 years of protecting the profession, advancing the status and shaping our futures”, wato tsayawa tare da malamai domin kare sana’ar koyarwa, inganta matsayinsu da kuma gina makomar gaba.
Kalu ya ce ya kamata malamai su samu albashin da ya dace da muhimmancin nauyin da ke kansu da kuma halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Ya tuna cewa gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta amince a shekarar 2022 da aiwatar da tsarin albashi na musamman ga malaman makarantun firamare da sakandare, tare da wasu tsare-tsaren inganta jin daɗinsu.
Sai dai ya ce duk da cewa shekaru huɗu sun shude tun bayan amincewar, har yanzu ba a fara aiwatar da tsarin ba.
NUT ta sabunta kiranta ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin fara aiwatar da sabon tsarin albashin malamai.
A cewar kungiyar, aiwatar da tsarin zai taimaka wajen ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa tare da inganta daraja da martabarsu a cikin al’umma.
Kalu ya kuma yi kira da a inganta yanayin aikin malamai, yana mai cewa ba za a yi tsammanin malamai za su gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba a wuraren da ke fama da cunkoson ɗalibai, ƙarancin kujeru da tebura da kuma rashin isassun kayan koyarwa.
An fara bikin Ranar Malamai ta Duniya ne a ranar 5 ga Oktoba, 1994, bayan amincewa da ita a taron International Conference on Education karo na 44 da aka gudanar a Geneva.
