Farfesa Anthony Kila ya musanta rahotannin da suka bayyana shi a matsayin “farfesa na ƙarya”, yana mai cewa wannan bayanin ba daidai ba ne, yana yaudarar jama’a kuma yana cutar da martabarsa da matsayinsa na ƙwararre.
Kila ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan wani rahoto da aka wallafa a ranar 3 ga Oktoba, 2026.
Ya ce har yanzu yana da matsayin farfesa, kuma yana tsaye kan cancantar ilimi da ƙwarewar da aka gina a kai wajen ba shi wannan mukami.
A cewarsa, “Don kauce wa shakku, ni farfesa ne, kuma ina tsaye kan wannan matsayi da kuma cancantar ilimi da ƙwarewar da aka gina a kai.”
Kila ya ce rahoton da aka wallafa ya samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin rashin cikakken fahimtar yanayin, asali da kuma tushen hukumomin da suka danganci matsayin farfesantakarsa.
Ya kara da cewa ya kamata a duba batun ne bisa sahihan bayanai da takardun da suka dace, yana mai cewa a shirye yake ya gabatar da takardun da suka shafi matsayin farfesantakarsa.
Kila, wanda shi ne Pro-Chancellor na Michael and Cecilia Ibru University da ke jihar Delta, sannan Daraktan Commonwealth Institute of Advanced and Professional Studies, ya kuma nuna rashin amincewarsa da amfani da kalmar “farfesa na ƙarya” wajen bayyana shi.
Ya ce wannan kalma an gabatar da ita ne kamar tabbataccen hukunci, lamarin da ya ce na iya yin mummunar illa ga martabarsa da matsayinsa na ƙwararre.
Kila ya ce ya yi mamakin irin yadda aka mayar da hankali a kansa, yana mai cewa ba ya riƙe da wani mukamin siyasa, kuma ba ya neman wani mukami na siyasa ko na gwamnati.
Sai dai ya amince da muhimmancin aikin jarida wajen binciken cancanta da tarihin mutanen da ke riƙe da muƙamai na alhaki. Amma ya ce irin wannan bincike ya kamata a gudanar da shi cikin adalci tare da cikakken fahimtar abubuwan da suka shafi lamarin.
Ya kuma gode wa abokan aikinsa, abokai, ɗalibai da sauran jama’ar da suka tuntube shi bayan wallafa rahoton, domin nuna masa goyon baya da amincewarsu da cancantarsa ta ilimi da ƙwarewa.
Martanin Kila ya biyo bayan wani rahoto na PREMIUM TIMES da ya yi zargin cewa Kila ya kasance yana gabatar da kansa a matsayin farfesa da kuma “Jean Monnet Professor of Strategy and Development” tsawon shekaru, duk da cewa jaridar ta ce ba ta samu hujjar cewa wata jami’a da aka amince da ita ce ta ba shi wannan matsayin na ilimi ba.
Rahoton ya ce Kila ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa European Centre for Advanced and Professional Studies, wadda ya ce tana Cambridge, United Kingdom, ce ta ba shi matsayin farfesantaka a shekarar 2016
