Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga Musulman Najeriya da su ƙara haɗa kai, riƙe addininsu da kuma kare ’yancin Musulmi na gudanar da ibadarsu ba tare da wani cikas ba.
Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis yayin taron babban zauren NSCIA da aka gudanar a ɗakin taro na Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki, musamman kasancewar an shafe kusan shekaru bakwai ba tare da gudanar da babban taron majalisar ba.
Sarkin Musulmin ya gode wa Allah da Ya ba da damar haɗuwar shugabannin Musulmi daga sassa daban-daban na ƙasar domin tattauna batutuwan da suka shafi al’ummar Musulmi da kuma ƙarfafa alaƙarsu a matsayin iyali guda.
Ya ce duk da cewa NSCIA ta ci gaba da gudanar da tarukan Kwamitin Babban Manufa na faɗaɗa, akwai wasu muhimman shawarwari da al’amura da ba za a iya gudanar da su ba sai an kira babban taron majalisar bisa ƙa’ida.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa rashin gudanar da babban taron na tsawon lokaci ya samo asali ne daga wasu ƙalubalen kuɗi, inda ya ce majalisar ta nemi tallafi domin samun damar ci gaba da gudanar da nauyin da ke kanta ga al’ummar Musulmi a faɗin Najeriya.
Ya kuma ce taron ya zo ne a lokacin da Najeriya da duniya ke fuskantar wasu ƙalubale, saboda haka ya kamata shugabannin Musulmi su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa tare da fahimtar irin nauyin da ke kansu.
A cewarsa, Musulmi ba za su kasance masu yin shiru ko zaman jiran a zo musu da matsalolin da suka shafi addininsu da jin daɗin al’ummarsu ba, sai dai su shiga cikin harkokin da suka dace domin kare muradun addininsu.
Sai dai Sarkin Musulmin ya jaddada cewa Musulunci bai yarda da tilasta wa mutum addini ba, yana mai cewa Musulmi ba sa neman tilasta wa kowa shiga addinin Musulunci.
Ya ce abin da Musulmi ke buƙata a Najeriya da sauran wurare shi ne a ba su damar gudanar da addininsu cikin ’yanci ba tare da tsangwama ba.
Ya kuma bayyana cewa akwai mutane da dama da suka rungumi Musulunci bisa son ransu, saboda haka ya zama wajibi ga Musulmi su tallafa musu tare da kare hakkinsu na gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci.
Bugu da ƙari, Sarkin Musulmin ya yi kira ga Musulmi da su kasance masu tawali’u da nuna daidaito, yana mai cewa dukkan mutane daidai suke a gaban Allah, kuma abin da ke bambanta mutum da wani shi ne tsoron Allah da kyawawan ayyuka.
Ya ce mafi darajar mutum a wajen Allah shi ne wanda ya fi kowa takawa.
Sarkin Musulmin ya kuma ƙarfafa gwiwar shugabannin Musulmi da sauran mambobin al’ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa al’umma hidima, ko a fili ko a ɓoye, yana mai cewa ba lallai sai mutum ya bayyana duk wani alheri da ya aikata ba kafin ya zama mai amfani.
A cewarsa, wasu daga cikin ayyukan da suka fi amfani ga addini da al’umma ana gudanar da su ne cikin shiru, ba tare da neman yabo ko samun suna ba.
A ƙarshe, Sarkin Musulmin ya gode wa mahalarta taron bisa halartar babban taron, yana mai fatan cewa tattaunawar za ta samar da sabbin hanyoyin ƙarfafa haɗin kan al’ummar Musulmi da ci gaban harkokin addini da al’umma.
