Ana fargabar cewa mutane uku sun rasa rayukansu sakamakon turmutsitsi da ya afku a harabar Gidan Gwamnatin Jihar Niger da ke Minna, a daren Talata, yayin da ɗaruruwan matasa da mata suka taru domin nuna goyon baya ga Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago.
Lamarin ya faru ne bayan shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ziyarci Gwamna Bago domin jajanta masa kan rasuwar mutane 37 da suka mutu sakamakon hatsarin aikin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Jita-jitar rabon kuɗi ta jawo cunkoso
Wani ganau ya bayyana cewa cunkoson jama’a ya fara ƙaruwa bayan yaɗuwar jita-jitar cewa Gwamnan zai raba kuɗi a harabar Gidan Gwamnati.
A cewar ganau, yawan mutanen ya ci gaba da ƙaruwa har zuwa misalin ƙarfe 10 na dare, inda lamarin ya ƙara rikicewa bayan Gwamna Bago ya fito domin yin magana da jama’ar da suka taru.
Sai dai an ce jama’ar sun kasa sauraron abin da yake faɗa saboda yawan cunkoso da hayaniya, lamarin da ya sa Gwamnan ya koma cikin Gidan Gwamnatin.
Har yanzu babu tabbacin hukuma kan mace-macen
Rahoton ya ce har zuwa lokacin da aka fitar da labarin, babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da mutuwar mutane uku.
Sai dai wani babban jami’in gwamnatin jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa wani lamari ya faru a Gidan Gwamnatin.
Jami’in bai bayyana adadin mutanen da suka mutu ko suka samu raunuka ba.
Hukumomin jihar ba su fitar da cikakken bayani kan abin da ya faru ba, yayin da ake jiran ƙarin bayani domin tabbatar da adadin waɗanda lamarin ya shafa.
