Kungiyar Nigerian Economic Summit Group (NESG) ta bayyana damuwa kan yadda ake samun gibin da ke kara fadada tsakanin tsarin ilimi a Najeriya da kuma bukatun kasuwar kwadago, tana mai cewa matsalolin da ke tattare da tsarin ilimin kasar na hana matasa samun kwarewar da za ta taimaka musu wajen samun ayyukan yi masu amfani.
Kungiyar ta ce ya kamata a daina auna ingancin tsarin ilimi da yawan takardun shaidar karatu da ake bayarwa kawai, a maimakon haka a mayar da hankali kan ko dalibai suna samun kwarewar da za ta kara musu amfani a wajen samar da ci gaban tattalin arziki da kuma biyan bukatun kasuwar aiki.
Shugaban bangaren Human Capital Development Thematic Group na NESG Community of Practice on Youth, Oluwatobi Oseni, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na gab da taron NESG na kasa, mai taken “Future-proofing Nigerian Education.”
Oseni ya ce babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta a fannin bunkasa jarin dan Adam ya samo asali ne daga abin da ya kira “karyewar tsarin ilimi”, wanda ya shafi matakan ilimi tun daga karatun farko har zuwa manyan makarantu, koyon sana’o’i da kuma samun damar shiga kasuwar aiki.
A cewarsa, matsalolin da ake samu a matakai daban-daban na tsarin ilimi na kara jawo wa juna matsala, yayin da Najeriya ke fama da dimbin yaran da ba sa zuwa makaranta, rashin ingantaccen ilimin karatu da lissafi a matakin farko, raguwar sakamakon jarabawa da kuma wahalar da matasa ke fuskanta wajen sauya ilimi zuwa aikin yi mai amfani.
Taron wanda aka shirya gabanin Taron Tattalin Arzikin Najeriya karo na 32, ya hada jami’an gwamnati, hukumomin ilimi, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin ci gaba domin tattauna batutuwan ingancin ilimi, samun damar yin karatu, bunkasa kwarewa da kuma shirya matasa domin aikin yi.
Shugabar Kwamitin Shirya NES#32, Ozofu Ogiemudia, ta ce samar da tsarin ilimi da zai dace da bukatun nan gaba na bukatar a mai da hankali kan dukkan matakan tsarin ilimi, tun daga karatun farko, samun damar shiga jami’a, tsarin manhaja, koyarwa, koyon kwarewa da kuma hanyar da dalibai ke bi daga makaranta zuwa kasuwar aiki.
Ta bukaci masu ruwa da tsaki su daina tsaya wa wajen gano matsaloli kawai, inda ta ce ya kamata a samar da hanyoyin magance matsalolin da za a iya aiwatar da su cikin sauki, samun kudin gudanarwa da kuma fayyace nauyin kowane bangare tare da auna sakamakon da aka samu.
Shi ma Babban Jami’in UNICEF mai kula da harkokin manufofin zamantakewa, Dr Moses Sichei, ya yi kira da a kara hada binciken da ake gudanarwa a jami’o’i da bukatun masana’antu.
Ya ce binciken da ake yi a matakin digiri na gaba, musamman na MBA, ya kamata ya mayar da hankali kan matsalolin da kamfanoni ke fuskanta a zahiri tare da samar da shawarwari da za su iya taimakawa wajen magance su, maimakon binciken ya tsaya a cikin dakunan karatu kawai.
Sichei ya kuma bukaci a kara hada harkokin kasuwanci, kirkire-kirkire da fasahar zamani cikin karatun jami’a, tare da samar da damar horon aiki, koyarwa daga kwararrun masana’antu da kuma kusantar da dalibai da masu aiki a fannonin da suke karantawa.
A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Hakeem Fawehinmi, ya ce akwai bukatar jami’o’i su kara karfafa hadin gwiwa da masana’antu domin su zama cibiyoyin kirkire-kirkire da bunkasa sana’o’i, baya ga ayyukansu na koyarwa, bincike da hidimar al’umma.
Ya ce binciken jami’a ya kamata ya samar da amfani kai tsaye ta hanyar sabbin dabaru, hujjojin da za su taimaka wajen tsara manufofi da kuma hanyoyin magance matsalolin da ke taimakawa wajen bunkasa masana’antu.
Fawehinmi ya kuma goyi bayan kara sanya koyar da harkokin kasuwanci cikin tsarin jami’a domin bai wa dalibai damar kirkirar ayyukan yi da kasuwancinsu, maimakon dogaro kawai da neman aikin gwamnati ko na kamfanoni.
Daraktar Shirye-shirye da Kawance ta British Council, Chikaodi Onyemerela, ita ma ta bukaci binciken ilimi ya mayar da hankali kan matsalolin da kamfanoni ke fuskanta tare da samar da hanyoyin magance su da za a iya amfani da su kai tsaye.
Ta kuma bukaci a karfafa Enterprise Development Centres a jami’o’i tare da kara mayar da hankali kan kirkire-kirkire, sabbin abubuwa da kuma rajistar mallakar fasaha a matsayin wasu daga cikin alamomin tasirin binciken jami’a.
A madadin Babban Sakataren Universal Basic Education Commission, Aisha Garba, Daraktar Koyar da Kwarewar Malamai, Maryam Sani-Rangaji, ta ce inganta ilimin firamare da sakandare na bukatar samar da ingantattun gine-ginen makarantu, kwararrun malamai da kuma ci gaba da kokarin mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin ajujuwa.
Ta kara da cewa ya kamata a kara mai da hankali kan yawan shigar yara makaranta, ci gaba da halarta, daga mataki zuwa mataki da kammala karatu, tare da inganta sakamakon ilimin farko da samar da isasshen kudin gudanar da ilimin bai daya.
NESG ta ce shawarwarin da aka samu daga taron tattaunawar za su taimaka wajen tsara manufofinta da fafutukanta gabanin NES#32, wanda aka shirya gudanarwa a Abuja a ranakun 26 da 27 ga Oktoba.
