Kasashen G4, wato Brazil, Jamus, Indiya da Japan, sun yi kira da a yi garambawul ga tsarin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC), suna cewa tsarin da aka kafa shekaru kusan 80 da suka gabata bai sake yin daidai da yanayin siyasar duniya na yanzu ba.
Ministocin kasashen hudu sun ce tsarin mambobin kwamitin na yanzu na fuskantar kalubale wajen wakiltar kasashen duniya yadda ya kamata, lamarin da suka ce ya shafi sahihancinsa, amincewar kasashe da kuma tasirinsa wajen tunkarar matsalolin zaman lafiya da tsaro a duniya.
Sun bayyana cewa, saboda yadda yanayin siyasar duniya ke kara rikicewa, bukatar sake fasalin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta zama mafi muhimmanci fiye da da.
G4 sun bukaci a kara yawan kujerun kwamitin, ta bangaren kujerun dindindin da kuma wadanda ba na dindindin ba, tare da kara wakilcin yankunan da ba su da isasshen wakilci ko kuma ba su da shi kwata-kwata.
Sun fi mayar da hankali kan yankunan Afirka, Asiya-Pacific da Latin Amurka da Caribbean, suna cewa rashin wakilcin wadannan yankuna ya samo asali ne daga wani tarihi na rashin daidaito.
Wannan batu na da muhimmanci musamman ga Afirka, domin nahiyar ba ta da ko daya daga cikin kujerun dindindin na Kwamitin Tsaro, duk da cewa tana da kujeru uku na wucin gadi.
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dade tana neman a bai wa nahiyar a kalla kujeru biyu na dindindin da kujeru biyar na wucin gadi, tare da irin hakkoki da damar da sauran mambobin dindindin ke da su, ciki har da damar amfani da veto idan aka ci gaba da tsarin veto.
Ministocin G4 sun kuma nuna damuwa kan yadda tattaunawar da aka shafe shekaru 18 ana yi tsakanin kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya ba ta haifar da wani gagarumin sakamako wajen kawo sauyi a Kwamitin Tsaron ba.
Sun soki gabatar da wata takardar da suka kira “bridging proposal”, suna cewa an gabatar da ita ne kafin a fara tattaunawar da za ta mayar da hankali kan rubutaccen tsarin sauyin.
A cewarsu, wannan shawara ba ta yi daidai da matsayin mafi yawan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da ke goyon bayan fadada Kwamitin Tsaron ta bangaren kujerun dindindin da wadanda ba na dindindin ba.
G4 sun bayyana cewa ba lallai ne a samu cikakkiyar yarjejeniya tsakanin dukkan kasashe ba kafin a dauki mataki kan batun sake fasalin Kwamitin Tsaro, inda suka yi nuni da tanade-tanaden Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
Kasashen hudu sun ce za su hada kai da sauran kungiyoyin da ke neman sauyi domin samar da wata shawara guda da za ta wakilci ra’ayin mafi yawan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya.
Sun kuma ce za su mayar da hankali wajen fara tattaunawar da za ta dogara da rubutaccen tsari, domin ganin an samu sauyi mai ma’ana a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
Haka kuma, G4 sun bayyana cewa bai kamata a takaita tattaunawar kan gyaran Kwamitin Tsaro ga tsarin Intergovernmental Negotiations kadai ba, inda suka nuna shirin yin amfani da wasu dandali, ciki har da babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
A watan Mayun 2026, Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya sake jaddada bukatar Afirka ta samu a kalla kujeru biyu na dindindin da biyar na wucin gadi a Kwamitin Tsaro.
G4 sun ce za su ci gaba da hada kai a yayin zaman taro na 81 na Majalisar Dinkin Duniya, yayin da jami’ai daga kasashen hudu za su ci gaba da bibiyar tattaunawar tare da duba ci gaban da aka samu a taron Daraktocin-Janar na gaba da za a gudanar a New Delhi.
