Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Asrah 24 TV
  • Education
  • Health
  • Podcast
  • Politics
  • Sports
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
Facebook X (Twitter) YouTube WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
ASRAH 24 MEDIA
Subscribe
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FTSE Russell Ta Mayar Da Najeriya Matsayin Frontier Market, NGX Ta Ce Wannan Sabon Farko Ne

    August 27, 2026

    CBN Ta Ce Sauye-Sauyen Tattalin Arziki Sun Kafa Tubalin Ci Gaba Da Daidaiton Arzikin Najeriya

    August 6, 2026

    KOTU TA SAMU MACE DA LAIFIN YUNKURIN KASHE ƳAR SHEKARA 9 BAYAN TA YAUDARE TA ZUWA DAJI

    June 26, 2026

    KOTU TA KI SAKIN SOWORE, TA DAGE YANKE HUKUNCI ZUWA 30 GA YUNI

    June 24, 2026

    Cuba Ta Yi Watsi Da Kalam an Trump Na Cewa Ƙasar Za Ta Faɗi

    September 22, 2026

    Trump Ya Kulla Yarjejeniyar Tsaro Da Greenland Da Denmark, Amurka Za Ta Gina Sansanonin Soji Biyu

    September 22, 2026

    NIS Ta Yi Rijistar ’Yan Najeriya 8,552 a Ƙasashen Waje, Birtaniya Ta Fi Yawan Masu Amfana

    September 21, 2026

    Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah-wadai da Kai Hari Kan Ofishinta a Libya

    September 8, 2026

    Hatsarin Jirgin NAF A Ondo: ’Yan Sanda Sun Ce Babu Wanda Ya Tsira, Ana Ci Gaba Da Neman Ragowar Jirgin

    October 6, 2026

    NAF Ta Tabbatar Da Hatsarin Jirgin Soji A Ondo, Mutane 32 Suna Ciki

    October 5, 2026

    Anthony Kila Ya Musanta Zargin Cewa Shi ‘Farfesa Na Ƙarya’ Ne

    October 5, 2026

    Jirgin Sojin Sama Ya Yi Hatsari A Kusa Da Naval Base A Igbokoda, Fasinjoji 25 Da Ma’aikata 7 A Ciki

    October 5, 2026
  • Asrah 24 TV
  • Education

    NUT Ta Koka Kan Rashin Aiwatar Da Albashin Musamman Ga Malamai

    October 5, 2026

    WAEC Ta Naɗa Suleiman Kum A Matsayin Sabon Shugaban Ofishin Najeriya

    October 4, 2026

    Yadda Ilimin Kyauta Na Awolowo Ya Sauya Rayuwata — Tsohon Kakakin JAMB

    October 4, 2026

    Gwamnatin Tarayya Za Ta Zaɓi Malamai 14 Domin Kyautar Shugaban Ƙasa

    October 4, 2026

    Jigawa Ta Dauki Sabbin Malamai 2,020 Domin Cike Gibin Ma’aikata A Makarantu

    October 2, 2026
  • Health

    APM Terminals Ta Bukaci Gaggauta Rage Fitar Da Hayakin Carbon A Bangaren Jiragen Ruwa

    October 4, 2026

    Enugu: An Zargi Wani Matashi Da Kashe Budurwarsa Bayan Rigima Kan HIV

    October 3, 2026

    Ranar Zuciya Ta Duniya: Wayar Da Kai Da Gwaji Da Wuri Na Taimakawa Wajen Kare Zuciya

    September 30, 2026

    Najeriya Ta Yi Wa ’Yan Mata Miliyan 18 Rigakafin HPV Domin Kare Su Daga Sankarar Mahaifa

    September 29, 2026

    Edo Ta Mayar Da Gwajin Da Maganin Zazzabin Cizon Sauro Kyauta A Asibitocin Gwamnati

    September 23, 2026
  • Podcast
  • Politics

    INEC Ta Ce Ba Za A Yi Zaɓen 2027 Da Ba A Kammala Ba

    October 6, 2026

    Gwamnatin Tarayya Ta Biya Bashin Fansho Na N758bn Da Ya Taru Tun 2007

    October 6, 2026

    Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Wadanda Suka Lashe Kyautar Malamai Da Makarantu Ta 2026

    October 6, 2026

    SSANU Ta Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 14 Kan Albashin Ma’aikata

    October 5, 2026

    Kotu Ta Tabbatar Da Gbenga Olawepo-Hashim A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Accord A 2027

    October 5, 2026
  • Sports

    Alcaraz Ya Lashe Gasar Japan Open Bayan Dawowa Daga Rauni

    October 6, 2026

    Japan Open: Alcaraz Ya Kai Ƙarshe Bayan Ya Doke Munar A Wasan Zafi

    October 5, 2026

    Kocin Spain Ya Goyi Bayan Lamine Yamal Ya Zama Fitaccen Jarumin Kwallo

    October 4, 2026

    Yamal Ya Ci Gaba Da Cin Kwallaye, Spain Ta Doke Czech Republic 3-1

    October 3, 2026

    Barcelona Ta Nemi A Dage Wasan Mata Da Real Madrid Saboda Ambaliyar Ruwa

    October 3, 2026
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
ASRAH 24 MEDIA
Home » Kungiyar Tarayyar Afirka Za Ta Kaddamar Da Sabuwar Hukumar Tantance Darajar Bashi A Oktoba
Business

Kungiyar Tarayyar Afirka Za Ta Kaddamar Da Sabuwar Hukumar Tantance Darajar Bashi A Oktoba

Asrah24 MediaBy Asrah24 MediaSeptember 2, 20263 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
African Union 1783091363 960x540

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sanar da cewa za a kaddamar da Hukumar Tantance Darajar Bashi ta Afirka (African Credit Rating Agency – AfCRA) a hukumance a ranar 7 ga Oktoba, 2026, a Port Louis, babban birnin Mauritius, inda hedkwatar hukumar take.

Kaddamar da hukumar na zuwa ne a matsayin wani muhimmin mataki da Afirka ke dauka wajen kara samun ‘yancin cin gashin kanta a harkokin kudi, musamman wajen yadda ake tantance karfin tattalin arzikin kasashen nahiyar da darajar basussukansu.

AU ta bayyana AfCRA a matsayin wani babban ci gaba wajen tabbatar da ikon Afirka na tsara labarinta na tattalin arziki da kuma rage dogaro da manyan hukumomin tantance darajar bashi na duniya.

Kungiyar ta ce tsawon shekaru, yadda ake kallon hadarin zuba jari a Afirka ya sanya kasashen nahiyar ke biyan karin kudin ruwa da ake kira “risk premium” wajen samun rance a kasuwannin duniya.

A cewar AU, AfCRA za ta samar da wata hanya ta tantance darajar bashi da ta fi la’akari da yanayin tattalin arzikin Afirka, juriyar tattalin arzikin kasashen nahiyar da kuma damar samun ci gaba.

Hukumar za ta kasance wata madadin ra’ayi ga manyan hukumomin tantance darajar bashi na duniya kamar Fitch Ratings, Moody’s Ratings da S&P Global Ratings.

Wannan shiri ya samo asali ne daga korafe-korafen da wasu gwamnatocin Afirka da masu tsara manufofi suka dade suna yi kan yadda ake tantance hadarin basussukan kasashen nahiyar.

Kasashe irin su Ghana da Zambia sun taba nuna damuwa kan yadda rage darajar bashin kasashensu ke kara musu tsadar samun rance tare da kara tsananta matsalolin basussuka.

Haka kuma, African Peer Review Mechanism (APRM) ta taba sukar Fitch Ratings kan yadda ta tantance African Export-Import Bank, inda ta zargi hukumar da rashin fahimtar yadda wasu cibiyoyin hada-hadar kudi na Afirka ke aiki.

Sai dai Fitch ta kare tsarin aikinta, tana mai cewa ratings dinta suna amfani da ka’idoji na duniya masu daidaito da kuma bayyana gaskiya.

Tun farko dai an shirya kaddamar da AfCRA ne a watan Satumba na 2025, amma daga baya aka dage shirin.

Domin kare martabarta da samun ‘yancin cin gashin kanta, hukumar ba za ta kasance mallakar gwamnatocin Afirka kai tsaye ba.

Ana kuma sa ran za ta fi mayar da hankali wajen tantance darajar takardun bashi da ake bayarwa a cikin kudaden kasashen Afirka.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce kaddamar da AfCRA zai nuna cewa Afirka na da karfin gina nata cibiyoyin kudi, tsara yadda duniya za ta fahimci tattalin arzikinta, da kuma samun karin iko kan makomarta ta fuskar kudi.

Ana sa ran kaddamar da hukumar a ranar 7 ga Oktoba, 2026, a Mauritius zai jawo hankalin kasashen Afirka da masu zuba jari, yayin da nahiyar ke kokarin sauya yadda ake kallon darajar tattalin arzikinta a kasuwannin duniya.

Share. Facebook Twitter Telegram WhatsApp
Previous ArticleShettima ya cika shekara 60, ya ce: “Kada ku kashe ko kwabo wajen sayen min kyauta”
Next Article ADC Ta Kafa Kwamitin Sulhu Don Sasanta Rikicin Zaben Fitar Da ‘Yan Takararta

Related Posts

CORAN Ta Bukaci Najeriya Ta Dakatar Da Shigo Da Man Fetur, Ta Mayar Da Ƙasar Cibiyar Tace Mai A Afirka

September 29, 2026

CCB Ta Binciki Kadarorin Ministoci Sama Da 20 Da Sakatarorin Gwamnati 30

September 23, 2026

Gidauniyar Dangote Za Ta Taimaka Wa Mata Miliyan Biyu Su Mallaki Hannun Jari A Matatar Dangote

September 22, 2026

Wike Ya Ce Ireti Kingibe Ba Za Ta Koma Majalisar Dattawa A 2027 Ba

September 22, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

Hatsarin Jirgin NAF A Ondo: ’Yan Sanda Sun Ce Babu Wanda Ya Tsira, Ana Ci Gaba Da Neman Ragowar Jirgin

October 6, 2026

INEC Ta Ce Ba Za A Yi Zaɓen 2027 Da Ba A Kammala Ba

October 6, 2026

Alcaraz Ya Lashe Gasar Japan Open Bayan Dawowa Daga Rauni

October 6, 2026

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Mutum Bayan Watanni Uku A Bauchi

October 6, 2026

Gwamnatin Tarayya Ta Biya Bashin Fansho Na N758bn Da Ya Taru Tun 2007

October 6, 2026
Connect with us
  • Facebook
  • Twitter
  • YouTube
  • WhatsApp
  • Instagram
  • TikTok
Top Posts
Advertisement
© 2026 ASRAH 24 MEDIA. Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.