Rundunar ’yan sandan jihar Kwara ta samu nasarar ceto Onigbesi na Igbesi, Oba Moses Omotayo, tare da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su kwanaki da suka gabata.
Rahotanni sun ce an sace Sarkin ne tare da mutanen biyu a ranar 22 ga Agusta, 2026, a garin Igbesi da ke ƙaramar hukumar Isin ta jihar.
An samu nasarar ceton su ne a yayin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar a yankin Elerin/Ijomu-Oro.
A cewar ’yan sandan, samamen ya biyo bayan wani rahoto da wani ɗan sa-kai ya kai ofishin ’yan sanda na Oro, inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikin mutanensa ya samu raunin harbin bindiga a hannu a cikin daji.
Jami’an ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai sun garzaya wurin, inda suka yi musayar wuta da masu garkuwar.
A yayin arangamar, an ce an hallaka ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin masu garkuwa ne, yayin da sauran suka tsere.
Daga bisani, jami’an tsaron suka ci gaba da bibiyar su, inda suka samu damar ceto Sarkin Igbesi da sauran waɗanda aka sace, wato Maryam Abubakar da Aisha Ilyasu.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta ci gaba da matsa kaimi wajen ganin an cafke sauran ’yan kungiyar da suka tsere, tare da tabbatar da tsaron al’ummar jihar.
Add A Comment
