Rundunar ’yan sandan jihar Lagos ta ce ta dawo da zaman lafiya a yankin Ikola, bayan wani rikici da ya barke a ranar Alhamis wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkatar wasu biyu.
Rahoton ya bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun tare wani mai tuka keke mai kafa uku, inda suka nemi ya ba su N200.
Bayan da direban ya ƙi biyan kuɗin, ana zargin mutanen sun kwace masa keken. Daga bisani direban ya dawo tare da wasu mutane, lamarin da ya rikide zuwa mummunan faɗa tsakanin ɓangarorin biyu.
A yayin rikicin, an kona wasu gine-gine, yayin da mutane uku suka rasa rayukansu, wasu biyu kuma suka samu raunuka.
Rundunar ’yan sandan ta ce an kai waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Sojoji da ke Yaba domin gudanar da abubuwan da suka dace.
Kwamishinan ’yan sandan Lagos, CP Tijani Fatai, tare da Kwamandan Brigade na 9 na Sojojin Najeriya, Brig. Gen. Afolabi Owolabi, sun ziyarci wurin domin duba halin da ake ciki da kuma daidaita matakan tsaro.
An kuma tura jami’an RRS, Task Force, Tactical Squad, PMF, Eko Strike Force da VCRU domin tabbatar da doka da oda.
’Yan sandan sun ce an fara bincike kan lamarin, kuma duk wanda aka samu da hannu a rikicin zai fuskanci hukunci bisa doka.
Rundunar ta kuma bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankula, su guji yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da taimakawa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen binciken.
