Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta bayyana cewa gasar TotalEnergies CAF Women’s Africa Cup of Nations (WAFCON) 2026 da za a gudanar a ƙasar Morocco na iya zama tarihi, inda ake sa ran karya wasu manyan tarihin gasar bayan an faɗaɗa ta zuwa ƙasashe 16.
A wata sanarwa da CAF ta fitar, ta bayyana manyan tarihin guda biyar da za su iya karyewa yayin gasar.
1. Gabrielle Onguéné na iya zama mafi yawan halartar WAFCON
Kyaftin ɗin Kamaru, Gabrielle Aboudi Onguéné, na iya zama ‘yar wasa mafi yawan halartar gasar WAFCON idan ta buga wasan ƙasarta da Mali. Idan hakan ta faru, za ta yi karo na takwas a gasar, ta zarce tsohuwar ‘yar wasan Najeriya Onome Ebi, wadda ta buga gasar sau bakwai.
2. Ordega da Ohale na neman kofi na shida
‘Yan wasan Najeriya Francisca Ordega da Osinachi Ohale na da damar ƙara kafa sabon tarihi idan Super Falcons ta kare kambunta. Su ne suka fi kowa lashe WAFCON da kofuna biyar, kuma za su iya ƙara shi zuwa shida.
3. Tarihin ƙwallo mafi sauri na iya karyewa
‘Yar wasan Tunisia Mariem Houij ce ke riƙe da tarihin ƙwallo mafi sauri a WAFCON bayan ta zura ƙwallo cikin daƙiƙa 17 kacal a gasar 2022. Sai dai CAF ta ce akwai yiwuwar wani ya karya wannan tarihi a gasar ta 2026.
4. Tarihin Perpetua Nkwocha na iya fuskantar barazana
Fitacciyar tsohuwar ‘yar wasan Najeriya Perpetua Nkwocha har yanzu tana riƙe da tarihin zura ƙwallaye 11 a gasa guda, wanda ta kafa a WAFCON ta 2010. Bayan shekaru 16, ana sa ran wata ‘yar wasa za ta iya karya wannan gagarumin tarihi.
5. Ana iya karya tarihin yawan ƙwallayen gasar
A gasar WAFCON ta 2024 an ci ƙwallaye 66, wanda shi ne mafi yawa a tarihi. CAF ta ce faɗaɗa gasar zuwa ƙasashe 16 zai ƙara yawan wasanni, lamarin da ke ƙara yiwuwar karya wannan tarihin.
CAF ta bayyana cewa sabon tsarin gasar ba kawai zai ƙara armashi ba ne, har ma zai ba da dama ga kafa sabbin tarihi da za su kasance abin tunawa a nahiyar Afirka.
