Kungiyar Daliban Jihar Ogun (NAOSS) ta soki zargin cewa tsohuwar Sanata Iyabo Obasanjo-Bello ta bukaci a mayar mata da kudaden da ta kashe wajen yakin neman zabe kafin zaben fidda gwani na gwamnan jam’iyyar APC a jihar.
Kungiyar ta bayyana cewa idan zargin gaskiya ne, hakan ya saba da ka’idojin siyasa mai nagarta, tare da nuna cewa siyasa ba kasuwanci ba ce da za a nemi dawo da kudin da aka kashe bayan kammala zabe.
NAOSS ta ce wannan batu ya fito ne bayan Sanata Solomon Olamilekan Adeola (Yayi) ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a zaben fidda gwani na shekarar 2027.
Kungiyar ta kara da cewa jawo dan takarar jam’iyyar cikin takaddamar kudi bayan zaben fidda gwani na iya haddasa rikici a cikin jam’iyyar tare da karkatar da hankali daga muhimman batutuwan da suka shafi al’ummar jihar Ogun.
NAOSS ta bukaci ‘yan siyasa da su rungumi siyasa mai tsafta da kishin jama’a maimakon mayar da ita hanyar neman riba.
