Shahararren mawakin Najeriya mai zama a Birtaniya, Speed Darlington, ya tayar da muhawara bayan ya bayyana cewa mutanen da suka kai shekaru 50 ba su da wani amfani da yin Japa (ƙaura zuwa ƙasashen waje domin neman rayuwa).
A cikin wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, mawakin ya ce mutane masu wannan shekaru ya kamata su sake tunani kafin su bar Najeriya, yana mai cewa lokacin da za su fara ganin amfanin wahalarsu a ƙasashen waje zai iya zama ya kure.
Ya ce yin ƙaura zuwa ƙasashen waje ya fi dacewa da matasa masu shekaru 20 zuwa sama, domin suna da ƙarin lokaci da ƙarfi na gina rayuwarsu.
Kalaman nasa sun sake jawo hankalin jama’a kan batun Japa, wanda ya dade yana haddasa muhawara a Najeriya, musamman bayan wasu fitattun mutane sun bayyana mabambantan ra’ayoyi game da rayuwa a ƙasashen waje.
