Wani masani kan harkokin mai da iskar gas, Victor Udoh, ya bayyana cewa shigo da kusan gangar danyen mai miliyan 39.9 da Matatar Dangote ta yi a watannin Mayu da Yuni kan kuɗin da ya kai dala biliyan $4.43, alama ce da ke nuna cewa shirin gwamnati na crude-for-naira bai cimma manufarsa ba.
Udoh ya bayyana hakan yayin wata hira da ARISE NEWS, inda ya ce da tsarin yana aiki yadda ya kamata, da matatar Dangote ba za ta kashe kusan dala biliyan biyar cikin watanni biyu wajen shigo da danyen mai daga ƙasashen waje ba.
Ya ce matatar ta shigo da gangar mai miliyan 21 a watan Mayu kan kuɗin dala biliyan $2.6, sannan ta sake shigo da gangar miliyan 18.9 a watan Yuni kan dala biliyan $1.83.
A cewarsa, wannan na nuna cewa har yanzu ba a samar wa matatar isasshen danyen mai a cikin gida ƙarƙashin tsarin crude-for-naira ba.
Udoh ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara yawan danyen man da take bai wa matatar Dangote a ƙarƙashin wannan tsari domin rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje, wanda zai taimaka wajen samar da mai cikin sauƙi da farashi mai rahusa ga ‘yan Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa matsalar ƙarancin samar da mai a Najeriya ta samo asali ne daga satar danyen mai da lalata bututun mai, yana mai cewa inganta tsaro ya taimaka wajen ƙara yawan man da ƙasar ke samarwa.
Sai dai ya jaddada cewa hukumomin da ke kula da harkokin mai dole ne su tabbatar da gaskiya da adalci wajen tsara farashin mai, tare da hana masu zuba jari anfani da kasuwa wajen cutar da masu amfani.
