Wani daga zuriyar gidan kayan ado na Cartier, mai suna Maximilien de Hoop Cartier, ya samu hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari na tarayya a Amurka bayan ya amsa laifin gudanar da haramtacciyar musayar kuɗin cryptocurrency da aka yi amfani da ita wajen wanke sama da dala miliyan 470 da suka samo asali daga fataucin miyagun ƙwayoyi.
Cartier, ɗan asalin Faransa mai shekaru 58 wanda kuma ke waka da sunan “Max Cartier”, an yanke masa hukunci ne a kotun tarayya da ke Manhattan ranar Talata, bayan ya amsa laifukan gudanar da kasuwancin kuɗi ba tare da lasisi ba da kuma haɗin baki wajen yaudarar bankuna.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa ya kafa wasu kamfanoni na bogi a Amurka, ciki har da Bullpix Solutions, Softmill LLC, da VC Innovated, waɗanda aka yi amfani da su wajen karɓa da tura kuɗaɗen miyagun ƙwayoyi zuwa Colombia.
An ce kamfanonin ba su da ainihin aiki, sai dai an ƙirƙire su ne don wanke kuɗaɗe ta hanyar canza cryptocurrency zuwa kuɗin ƙasa.
Domin ya ɓoye gaskiya daga bankuna, Cartier ya yi amfani da takardun bogi da kwangiloli na ƙarya yana nuna cewa kamfanonin suna yin harkar fasaha da software. Haka kuma, ya raba kuɗaɗe zuwa ƙananan sassa domin kauce wa binciken bankuna.
Hukumar bincike ta Amurka (FBI) ta bayyana wannan tsarin a matsayin “Cartier Cell”, wanda aka ce ya fara aiki tun a shekarar 2018.
Rahotanni sun ce Cartier ya shaida wa wani jami’in FBI da ke ɓoye cewa yana amfani da wani otal a New York a matsayin “gida na biyu” inda yake gudanar da harkokinsa na crypto da hulɗa da abokan ciniki.
A shekarar 2021, hukumar DEA ta ƙwace kusan dala 940,000 daga asusunsa a wani aikin sirri da aka yi domin gano hanyar kuɗaɗen miyagun ƙwayoyi.
Bayan haka, Cartier ya kai takardun bogi ofishin Lauyan Gwamnatin Amurka a Pennsylvania yana neman a mayar masa da wasu kuɗaɗen, kafin bincike ya fallasa cikakken tsarin laifin da ya haifar da hukuncin da aka yanke masa.
An kuma umarce shi da ya biya dala 2,362,160 a matsayin kuɗin da aka samu daga laifin, tare da kwace wasu asusun banki na kamfanonin bogin da ya kafa.
Lauyan gwamnatin Amurka, John Clayton, ya ce Cartier ya yi amfani da iliminsa na tsarin kuɗi na Amurka da na ƙasashen waje wajen taimaka wa masu fataucin miyagun ƙwayoyi wanke kuɗaɗensu.
