Dan wasan bayan Ipswich Town, Ashley Young, ya sanar da cewa zai iya yin ritaya daga kwallon kafa ta ƙwararru bayan shafe shekaru 23 yana buga wasa, yana mai cewa wasan da za a buga a mako mai zuwa na iya zama na ƙarshe a rayuwarsa ta kwallon kafa.
Young ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X (Twitter), inda ya ce tafiyarsa a wasan ƙwallo ta kasance abin alfahari da mafarki da ya cika.
Ya ce ya taka leda a manyan filayen wasa a Ingila da Turai, ciki har da Wembley, Old Trafford, San Siro, Villa Park da Portman Road, yana mai cewa:
“Daga Sefton Road zuwa Vicarage Road zuwa Villa Park zuwa Wembley zuwa Old Trafford zuwa San Siro… tafiya ce da ban taɓa tunanin zan samu ba tun ina yaro.”
Dan wasan mai shekaru 39 ya kuma ce akwai yiwuwar wasan da zai buga a ranar Asabar ya zama na ƙarshe a rayuwarsa ta ƙwararru.
“Amma kowace mafarki tana da ƙarshe, kuma Asabar na iya zama wasan ƙarshe na rayuwata a ƙwallon kafa. Shekaru 23 kuma an gama,” in ji shi.
Kungiyoyin da ya taɓa bugawa, musamman Aston Villa da Everton, sun yaba masa bisa irin gudummawar da ya bayar a tsawon shekaru.
Aston Villa ta ce ya buga wasanni 250 tare da zura ƙwallaye 40, tana mai kiransa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasanta na zamani.
Everton kuma ta taya shi murna bisa “kyakkyawan aiki da ya yi a rayuwarsa ta ƙwallo”.
Ashley Young ya fara aikinsa ne a farkon shekarun 2000, inda ya taka leda a manyan kulab-kulab kamar Manchester United da Inter Milan, kafin daga bisani ya koma Ingila ya ci gaba da taka leda har zuwa matakin ƙarshe na aikinsa.Ashley Young Ya Bayyana Yiwuwar Yin Ritaya Bayan Shekaru 23 a Kwallon Kafa
