Pakistan na ci gaba da yin muhimman tattaunawar sirri (back-channel diplomacy) domin ƙoƙarin warware takaddama tsakanin Amurka da Iran, a daidai lokacin da tattaunawar da ake yi a fili ta tsaya cik, in ji wasu majiyoyin gwamnatin Pakistan.
Rahoton ya bayyana cewa Pakistan na aiki a ɓoye ne domin samar da wata sabuwar dabara ko “new formula” wacce za ta taimaka wajen cimma yarjejeniya kan manyan batutuwa guda biyu da ke rikita dangantakar ƙasashen, wato:
Batun Shataletalen Hormuz (Strait of Hormuz) da ke da muhimmanci wajen jigilar mai a duniya
Da kuma shirin nukiliyar Iran
Majiyoyin sun ce bangarorin biyu (Amurka da Iran) na ci gaba da musayar saƙonni ta hanyar Pakistan, inda ake gabatar da shawarwari da kuma martani domin neman mafita.
