Fitaccen mai shirya waka kuma Shugaban kamfanin Mavin Records, Don Jazzy, ya bayyana cewa yawan kasancewarsa a kafafen sada zumunta ba kawai nishaɗi ba ne, illa wata dabara ce ta neman sabbin hazakar waka, duk da cewa mutane da dama kan fahimci hakan ba daidai ba.
Don Jazzy ya ce kasancewarsa a soshiyal mediya, musamman bin matasa mata masu kyau da salo (Gen Z), ana yawan fassara shi ba daidai ba, alhali hakan na daga cikin hanyoyinsa na gano sabbin hazaka.
Ya ce:
“Mutane suna cewa ina bin ‘Gen Z baddies’ da yawa a Instagram, amma hakan ne ma ya taimaka min wajen gano Ayra Starr,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa sau da yawa yana roƙon matasa su tura masa shafukan abokansu da suke da hazaka domin ya duba su.
Shugaban Mavin Records ya ƙara da cewa a wasu lokuta yana tuntuɓar sabbin hazaka kai tsaye bayan ya hango su, har ma yana iya tuntuɓar iyayensu domin tabbatar da hanyar sadarwa idan ya cancanta.
Ya ce soshiyal mediya ta zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyinsa na gano sabbin mawaka a ‘yan shekarun nan, inda ya ce yawancin wadanda ya ɗauka aiki sun fito ne daga irin wannan bincike na kan layi, musamman matasa masu ƙirƙirar abun ciki.
A cewarsa, babbar nasarar da ya samu a wannan hanya ita ce gano fitacciyar mawakiyar nan Ayra Starr, wadda ya gano ta ne a Instagram kafin ta shahara a masana’antar waka.
