Presidential Enabling Business Environment Council (PEBEC) ta umarci dukkan Ma’aikatun Gwamnati, Sassa, da Hukumomi (MDAs) da su dakatar da gabatar da sabbin manufofi da dokoki domin kaucewa kawo cikas ga harkokin kasuwanci a kasar nan.
Wannan umarni ya fito ne cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na PEBEC, Zahrah Mustapha-Audu, ta fitar a ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin gwamnati na samar da yanayi mai sauki ga ‘yan kasuwa, musamman a wannan lokaci da tattalin arziki ke fuskantar matsin lamba.
PEBEC ta jaddada cewa sabbin dokoki ko sauye-sauye a tsarin gudanarwa na iya haifar da tangarda ga harkokin kasuwanci, wanda hakan zai iya rage zuba jari da kuma kawo tsaiko ga ci gaban tattalin arziki.
Majalisar ta bukaci MDAs su mayar da hankali wajen inganta aiwatar da dokokin da ake da su a yanzu, maimakon kara sabbin ka’idoji da ka iya dagula harkokin kasuwanci.
Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen karfafa gwiwar masu zuba jari da kuma bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
