Yarima Harry da matarsa Meghan Markle sun koma Birtaniya bayan shafe shekaru shida da ficewa daga ayyukan gidan sarautar Birtaniya.
Rahotanni sun ce komawar tasu na da nasaba da wasu dalilai, ciki har da damar da Meghan ta samu na komawa harkar fim a wata shirya-shirya da ake dauka a Birtaniya.
‘Ya’yansu biyu, Archie da Lilibet, an kuma ruwaito cewa an sanya su a wata makaranta a Birtaniya, yayin da ma’auratan suka zabi sabon gida.
Sai dai masana na ganin cewa komawar Meghan Birtaniya na iya zama babban kalubale, musamman ganin yadda har yanzu ba ta da farin jini sosai a kasar.
A wani sabon binciken YouGov da aka fitar a watan Yuli, kashi 65 cikin 100 na mutanen Birtaniya sun bayyana ra’ayi mara kyau game da Meghan.
Harry da Meghan sun taba yin kakkausar suka ga kafafen yada labarai na Birtaniya, inda Meghan ta ce duk kokarin da ta yi na ganin ta samu karbuwa bai hana wasu daga cikin kafafen yada labarai kokarin bata mata suna ba.
Sai dai masana sun ce a wannan karon, Harry da Meghan ba su koma Birtaniya ne domin sake shiga rikici da gidan sarauta ba, illa dai neman kwanciyar hankali da kyakkyawar makoma ga iyalinsu da ‘ya’yansu.
