An tabbatar da rasuwar fitaccen mai hawan duwatsu kuma tsohon jami’in rundunar musamman ta Birtaniya, Nirmal “Nimsdai” Purja, bayan wata mummunar ambaliyar kankara da ta afku a dutsen Broad Peak da ke arewacin Pakistan.
Purja, wanda ya kafa kamfanin Elite Exped, yana jagorantar wata tawaga ta mutane 10 lokacin da ambaliyar kankarar ta rutsa da su da misalin tsakar rana ranar Alhamis.
A cewar Alpine Club of Pakistan, babu wani daga cikin tawagar da ya tsira daga hatsarin.
A cikin wata sanarwa da kamfanin Elite Exped ya wallafa a shafinsa na Instagram, an bayyana rasuwar Purja da sauran abokan hawan duwatsun nasa cikin matuƙar alhini.
Sanarwar ta kuma tabbatar da rasuwar abokan tafiyarsa Pur Bahadur Gurung (Yukta) da Nima Sherpa, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansu da duk waɗanda abin ya shafa.
Masu aikin ceto sun fara bincike bayan aukuwar hatsarin, inda suka gano gawarwakin mutane huɗu, ciki har da Nadhira Al Harthy daga ƙasar Oman da kuma Pur Bahadur Gurung daga Nepal.
Marigayi Nirmal Purja mai shekaru 43, ɗan asalin Nepal ne da ya zama ɗan ƙasar Birtaniya, kuma ya shahara a duniya wajen hawan manyan duwatsu.
A shekarar 2019, ya kafa tarihi bayan ya hau kololuwar duwatsu 14 mafi tsawo a duniya cikin watanni shida kacal, abin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin fitattun masu hawan duwatsu a tarihi.
Haka kuma, wannan bajintar tasa ta zama jigon shirin fim na Netflix mai suna “14 Peaks: Nothing Is Impossible”, wanda ya nuna yadda ya yi nasarar cin galaba kan manyan duwatsu masu haɗari a duniya.
