Shahararren mawaƙin Najeriya, Portable, ya sake shan kaye a wasan damben fitattun mutane bayan an kori shi daga fafatawar da ya yi da jarumin Nollywood, Charles Okocha, a daren Juma’a a birnin Legas.
Wasan, wanda aka yi wa lakabi da “Unfinished Business”, ya kasance karo na biyu tsakanin Portable da Okocha, bayan cece-kuce da suka biyo bayan haduwarsu ta farko.
A yayin fafatawar, Portable ya nuna ƙwazo a farkon wasan, amma daga baya damben ya rikide zuwa jan-in-ja da kama juna, lamarin da ya sa alkalin wasa ya kasa raba su.
Bayan kararrawar ƙarshen zagaye ta buga, jami’an tsaro da masu gadin ‘yan wasan suka shiga tsakani domin raba su. Sai dai Portable ya fita daga cikin zoben dambe kafin alkalin wasa ya yanke hukunci, abin da ya jawo magoya baya suka fara yi masa ihu.
Daga bisani an dawo da shi cikin zoben, inda alkalin wasa ya sanar da cewa an kore shi daga fafatawar, wanda hakan ya bai wa Charles Okocha nasara.
Kafin fara wasan, Portable ya bayyana cewa yana addu’ar Allah Ya ba shi farin ciki tare da iyalansa.
Wannan shi ne karo na biyu cikin watanni uku da Portable ke shan kaye a damben fitattun mutane, bayan ya sha kashi a hannun Carter Efe a watan Mayun bana.
A sauran wasannin da aka gudanar a daren, an samu nasarori da dama ta hanyar bugun knockout, yayin da wasu fafatawa suka kare da hukuncin alkalai. Haka kuma, wasan tsakanin mawaka Idowest da Mr Real ya kare babu wanda ya yi nasara.
An gudanar da taron damben ne a Balmoral Convention Centre da ke Victoria Island, Legas, inda dubban masoya suka halarta domin kallon fafatawar.
