Birnin East Orange da ke jihar New Jersey a Amurka ya ƙulla haɗin gwiwa da Ugwumba Leadership Centre for Africa domin bunƙasa horar da shugabanni, haɓaka ƙwarewar ɗan Adam da kuma ƙarfafa matasa a Najeriya da Amurka.
An sanar da wannan haɗin gwiwa ne bayan wata ganawa tsakanin Magajin Garin East Orange, Ted Green, da wanda ya kafa cibiyar Chief Uche Nwosu, a jihar New Jersey.
A cewar ɓangarorin biyu, haɗin gwiwar zai mayar da hankali kan horas da shugabanni, koyar da sana’o’i da ƙwarewa, musayar ilimi da kuma aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’umma a ƙasashen biyu.
Magajin Garin East Orange, Ted Green, ya bayyana cewa manufar haɗin gwiwar ita ce ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin birnin da Najeriya ta hanyar shirye-shiryen da za su bunƙasa shugabanci da jarin ɗan Adam, tare da samar da sabbin damar haɗin kai tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu.
A yayin taron, Green ya bai wa Chief Uche Nwosu lambar yabo ta Outstanding Leadership and Human Capacity Development, tare da ba shi tambarin hukuma na birnin East Orange, domin karrama gudummawar da yake bayarwa wajen haɓaka shugabanci da ci gaban matasa.
Da yake mayar da martani, Nwosu ya gode wa Magajin Garin da al’ummar East Orange bisa wannan girmamawa, yana mai cewa hakan zai ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen faɗaɗa shirye-shiryen bunƙasa shugabanci da ƙarfafa matasa.
Ya ce, “Wannan haɗin gwiwa yana nufin saka hannun jari a cikin mutane. Zai ba mu damar haɓaka shugabanni, ƙarfafa matasa da samar da damammakin da za su amfani al’ummominmu na dogon lokaci.”
Nwosu ya kuma bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin al’ummomin Najeriya da Amurka ta hanyar shirye-shiryen horaswa da gina ƙwarewa.
Har ila yau, ya yabawa membobin tawagarsa da suka haɗa da Kings Umege, Chief Ewhoma Tony Okpokparoro, Prince Anozie Ugenyi da Kizito Umege bisa goyon bayan da suka bayar wajen nasarar ziyarar.
Cibiyar Ugwumba Leadership Centre for Africa ta ce za ta jagoranci aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi bunƙasa shugabanci, ƙarfafa matasa, koyar da sana’o’i da ci gaban al’umma mai ɗorewa a Najeriya dkoa Amurka.