Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta buɗe binciken ladabtarwa kan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Argentina bayan rikicin da ya barke tsakanin ‘yan wasan Argentina da na Spain bayan wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya.
An fara binciken ne bayan Argentina ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Spain a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na New York New Jersey Stadium.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan wasan Argentina da jami’an tawagar sun shiga sa-in-sa da ‘yan wasan Spain bayan an busa ƙarshen wasa.
FIFA ta ce za ta binciki ‘yan wasan Nahuel Molina da Leandro Paredes, tare da mataimakin koci Roberto Ayala, kan zargin cin zarafi da amfani da tashin hankali, yayin da kuma ake binciken Molina, Thiago Almada da ɗan wasan Spain Gavi kan zargin rashin ɗa’a a filin wasa.
Baya ga haka, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Argentina (AFA) ita ma na fuskantar bincike kan wasu zarge-zarge da suka haɗa da nuna wariya, kalaman cin mutunci, karya dokokin tsaro da kuma amfani da wasanni wajen isar da saƙonnin siyasa.
Haka kuma FIFA za ta binciki tutar da ‘yan wasan Argentina suka nuna bayan nasarar da suka samu a wasan kusa da na ƙarshe, wadda ke goyon bayan ikirarin ƙasar kan tsibiran Falkland (Las Malvinas).
FIFA ta ce za ta tantance dukkan hujjoji kafin yanke hukunci kan matakan ladabtarwa da za a ɗauka kan ‘yan wasan, jami’an ƙungiyar da kuma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Argentina.
