Hukumar NASENI (National Agency for Science and Engineering Infrastructure) ta bayyana cewa ta samar da kayayyaki sama da 44 da aka ƙera a Najeriya masu ingancin kasuwa, tare da ƙirƙirar fiye da ayyukan yi 30,000 kai tsaye da kuma a kaikaice a shekarar 2025.
Shugaban hukumar, Khalil Suleiman Halilu, ya bayyana hakan yayin bikin karrama ma’aikatan NASENI na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce daga cikin kayayyakin da hukumar ta ƙera akwai kwamfutocin tafi-da-gidanka (laptops), wayoyin hannu, famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana da kuma baburan adaidaita sahu masu amfani da lantarki (electric tricycles).
Halilu ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gina NASENI Solar Industrial Park a jihar Nasarawa, wanda ake sa ran zai zama cibiyar ƙera kayayyakin makamashi mai tsafta mafi girma a nahiyar Afirka.
Haka kuma ya ce hukumar ta ba mata injiniyoyi tallafin sama da Naira miliyan 229 domin ƙarfafa bincike da kirkire-kirkire, tare da jaddada cewa shirye-shiryen NASENI sun taimaka wajen bunƙasa fasaha da samar da guraben aikin yi a Najeriya.
