Masana kan cutar daji sun yi kira ga al’umma da su rika kula da duk wani kumburi ko ciwon ƙashi da ba ya warkewa, suna mai gargadin cewa hakan na iya zama alamar cutar Sarcoma, wata nau’in cutar daji mai wuya da ke shafar ƙashi da sauran sassan jiki masu haɗa nama.
Wata ƙwararriyar likita kan cutar daji ta bayyana cewa Sarcoma na iya tasowa a tsokoki, kitse, jijiyoyin jini, gaɓoɓi, guringuntsi da sauran sassan da ke tallafawa jiki, kuma tana iya kamawa yara da manya.
Ta ce sau da yawa ana rikita alamomin cutar da wasu ƙananan cututtuka, lamarin da ke jinkirta gano ta da kuma fara magani a kan lokaci.
Likitar ta shawarci duk wanda ya lura da:
Kumburi da ba ya gushewa,
Wani ƙulli a jiki,
Ciwon ƙashi mai ɗaukar lokaci,
Ko ƙulli da ya fi santimita biyar girma,
da ya garzaya cibiyar lafiya mafi kusa domin a duba lafiyarsa.
Ta kuma buƙaci ma’aikatan lafiya su kasance masu lura da irin waɗannan alamomi domin a gano cutar tun da wuri tare da tura marasa lafiya zuwa cibiyoyin ƙwararru.
Masaniyar ta bayyana cewa maganin Sarcoma na buƙatar haɗin gwiwar ƙwararrun likitoci daban-daban, ciki har da likitocin tiyata, likitocin cutar daji, ƙwararrun hasken magani, masu gwaje-gwaje da sauran jami’an lafiya.
Ta yi kira ga gwamnati, cibiyoyin lafiya, ƙungiyoyin fararen hula da kafafen yaɗa labarai da su ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin gano cutar da wuri da kuma inganta samun ingantaccen magani.
An bayyana cewa ana gudanar da Watan Wayar da Kan Jama’a Kan Cutar Sarcoma a duk duniya a watan Yuli domin ƙara ilimantar da al’umma game da cutar da kuma ƙarfafa gano ta da wuri.
