Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa kusan kashi 45 cikin 100 na cutar dementia ana iya hana ta ko kuma a jinkirta bullarta idan aka rage abubuwan haɗari da suka shafi salon rayuwa da muhalli.
A cikin sabbin ƙa’idojin da hukumar ta fitar, WHO ta ce abubuwa kamar shan taba sigari, yawan shan barasa, rashin motsa jiki, gurɓacewar iska, keɓance kai daga jama’a, hawan jini da ciwon sukari na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da cutar.
Hukumar ta bayyana cewa dementia ita ce ta bakwai cikin manyan cututtukan da ke haddasa mace-mace a duniya, tare da janyo nakasa da dogaro ga wasu musamman a tsakanin tsofaffi.
A cewar WHO, sama da mutane miliyan 57 na rayuwa da cutar dementia a faɗin duniya, yayin da ake samun kusan sabbin mutane miliyan 10 da ke kamuwa da ita a kowace shekara.
Hukumar ta kuma ce cutar Alzheimer’s ita ce mafi yawan nau’in dementia, inda take da kaso tsakanin 60 zuwa 70 cikin 100 na duk masu fama da cutar.
Daraktar Sashen Cututtukan da Ba Su Yaɗuwa da Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta WHO, Devora Kestel, ta ce cutar ba ta shafi marasa lafiya kaɗai ba, har ma da iyalansu da al’ummarsu.
WHO ta ƙara da cewa, duk da cewa har yanzu ba a gano maganin warkar da dementia ba, ɗaukar matakan kariya tun da wuri da kula da lafiya na iya rage yawan masu kamuwa da ita tare da inganta rayuwar al’umma.
