Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Enugu ta kwace motoci 195 bisa zargin karya dokokin rajistar ababen hawa da amfani da lambobin mota da ba su cika ka’ida ba.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Daniel Ndukwe, ya fitar bayan wani samame na musamman da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Mamman Giwa, ya jagoranta.
A cewar rundunar, an kwace motocin ne saboda rashin rajista, amfani da lambar mota guda daya maimakon biyu, da kuma amfani da lambobin da aka rufe, aka gurbata, aka boye ko aka daura ba bisa ka’ida ba.
Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da duk masu motocin da aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.
Kwamishinan ‘Yan Sandan ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gargadin cewa za a ci gaba da aiwatar da wannan sintiri domin tabbatar da bin dokokin rajistar motoci.
Ya kuma tunatar da umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, na tilasta bin dokar hana zirga-zirgar motocin da ba su da rajista ko kuma masu amfani da lambobin da ba su dace ba.
Rundunar ta ce irin wadannan laifuka na iya zama barazana ga tsaro, saboda ana yawan amfani da motocin da ba su da cikakkiyar shaida wajen aikata laifuka. Haka kuma, an gargadi jami’an ‘yan sanda da su guji cin zarafin jama’a ko karbar rashawa yayin gudanar da aikin.
