Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya naɗa Martin Anayochukwu Oli a matsayin Kwamishina da aka gabatar, lamarin da ya sa ya zama mutum na biyu da ba ɗan asalin jihar Edo ba da aka ba muƙamin gwamnati tun bayan hawan gwamnan kan mulki.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Patrick Ebojele, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce wannan naɗin ya nuna aniyar gwamnatin Okpebholo na gina gwamnati mai bai wa kowa dama ba tare da la’akari da ƙabila ko asali ba.
Sanarwar ta ce Martin Oli, ɗan asalin ƙaramar hukumar Aninri ta Jihar Enugu, ɗan kasuwa ne kuma jagoran al’umma da ya yi fice wajen ayyukan ci gaban al’umma a tsakanin al’ummar Igbo mazauna Edo.
Ta kuma bayyana cewa wannan shi ne babban naɗi na biyu da aka bai wa wanda ba ɗan asalin Edo ba, bayan naɗin Abdulkarim Kadiri, jagoran al’ummar Hausawa/Fulani a Edo, a matsayin Mai Bai Wa Gwamna Shawara Kan Harkokin Al’umma a watan Nuwamban 2024.
A cewar gwamnatin jihar, Edo na ɗauke da al’ummomi daban-daban da suka haɗa da Igbo, Hausa/Fulani, Yarbawa da sauran ƙabilu, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki da ci gaban jihar.
Gwamnatin ta ce naɗin Oli ya nuna cewa ƙwarewa, jajircewa da hidimar al’umma ne ake la’akari da su wajen zaɓen masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Za a miƙa sunansa gaban Majalisar Dokokin Jihar Edo domin tantancewa da tabbatar da naɗin bisa tanadin doka.
