Iyalan marigayiyar fitacciyar mawakiyar Amurka, Whitney Houston, sun fito sun karyata ikirarin da fitacciyar mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, Oprah Winfrey, ta yi cewa mawakiyar tana karkashin tasirin miyagun kwayoyi lokacin da ta halarci shirinta a shekarar 2009.
Iyalan mawakiyar, karkashin jagorancin Pat Houston, sun fitar da sanarwa suna mayar da martani ga kalaman da Oprah ta yi a taron Cannes Lions da aka gudanar a kasar Faransa.
A cewar Oprah, Whitney ta sake komawa amfani da miyagun kwayoyi a lokacin, har ma ta fadi daga dandali yayin wata ziyararta ta karshe zuwa shirin nata. Ta kuma ce ta roki masu kallo kada su dauki hotuna ko yada lamarin domin kare martabar mawakiyar.
Sai dai Pat Houston ya bayyana cewa lallai Whitney ta fadi daga wani dandali, amma hakan ya faru ne lokacin gwajin sauti (sound check) saboda duhun wurin da kuma rashin saba da tsarin dandalin.
Sanarwar ta ce, “Whitney ta fadi daga dandali, amma hakan ya faru ne yayin gwajin sauti saboda duhun wurin da kuma rashin sanin yadda aka tsara dandalin. Ba ta kasance karkashin tasirin miyagun kwayoyi ba.”
Iyalan sun amince cewa Whitney ta yi fama da matsalar shaye-shaye a wasu lokuta na rayuwarta, amma sun ce bai dace a danganta duk wani abu da ya same ta da wannan matsala ba.
Sun kara da cewa abin da masu kallo suka gani a kan dandali a lokacin ya samo asali ne daga jajircewa, baiwa da kwazon mawakiyar, ba daga hasashe ko zarge-zargen da wasu ke yi ba.
Lamarin ya sake tayar da muhawara tsakanin masoya mawakiyar da masu bibiyar tarihin rayuwarta, musamman bayan sabbin kalaman da Oprah Winfrey ta bayyana game da shekarun karshe na rayuwar Whitney Houston
