Hukumar Kula da Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) ta kama wani dan Najeriya mai suna Ayodeji Olamide Ajayi bayan an same shi da laifuffuka da dama masu nasaba da tashin hankali.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar 22 ga Yunin 2026, ta bayyana cewa Ajayi na fuskantar korar gaggawa zuwa Najeriya bayan kammala matakan doka da suka dace.
Bayanan shige da fice sun nuna cewa Ajayi ya shiga Amurka ne a shekarar 2007 da takardar izinin karatu. Sai dai daga baya ya daina karatunsa kuma bai bar kasar ba, lamarin da ya sa ya ci gaba da zama a kasar ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ICE ta ce yayin zamansa a Amurka, Ajayi ya tara tarihin laifuffuka da suka hada da cin zarafin iyali, shiga harabar wasu ba tare da izini ba, barazana da kuma hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu.
Rahotanni sun kuma nuna cewa an taba danganta shi da manyan zarge-zarge da suka hada da garkuwa da mutane, fyade da kuma sakaci da iyali.
A shekarar 2024, Hukumar Sheriff ta Hamilton County da ke jihar Tennessee ta fara farautarsa bayan ana nemansa ruwa a jallo kan wasu manyan laifuka da suka hada da fyade mai tsanani sau hudu da kuma shiga gida da karfi.
Daga bisani jami’an tsaro sun gano shi a Bradley County inda aka yi doguwar tattaunawa da shi bayan ya yi barazanar cewa zai tilasta jami’an tsaro su kashe shi, yana ikirarin cewa yana dauke da bindiga.
Sai dai bayan ya mika kansa cikin lumana, an gano cewa abin da yake rike da shi ba bindiga ta gaske ba ce, illa wata bindigar wasan yara mai suna BB pistol.
Hukumar ICE ta ce matakin korarsa wani bangare ne na kokarin gwamnatin Amurka na korar bakin haure da suka aikata manyan laifuka daga kasar.
