Shugaban Hukumar Kula da Taswirar Ruwa ta Kasa (NHA), Rear Admiral Olumide Fadahunsi, ya bayyana cewa tattarawa da rarraba sahihan bayanai kan tekuna da hanyoyin ruwa na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa, kare muhalli da bunkasa tattalin arzikin ruwa a Najeriya.
Fadahunsi ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin taron manema labarai na bikin Ranar Hydrography ta Duniya ta shekarar 2026, inda ya jaddada bukatar Najeriya ta inganta yadda take adanawa da musayar bayanan tekuna domin cin gajiyar damar da ke cikin tattalin arzikin ruwa.
Ya ce sahihan taswirorin ruwa da bayanan da ake samu daga binciken zamani suna taimakawa wajen samar da tsaro ga jiragen ruwa, bunkasa tashoshin jiragen ruwa, gudanar da ayyukan makamashi a teku, kamun kifi da kuma kare gabar teku daga barazanar sauyin yanayi.
A cewarsa, Najeriya za ta gudanar da babban bikin ranar a Legas ranar 20 ga watan Yuni, inda masana, jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki za su tattauna hanyoyin inganta amfani da bayanan tekuna domin bunkasa kasuwanci da tsaron hanyoyin ruwa.
Ya kara da cewa inganta tsarin bayanan teku zai rage hadurran ruwa, karfafa harkokin kasuwanci ta ruwa da kuma taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa.
Fadahunsi ya bukaci karin hadin gwiwa tsakanin hukumomi, masana da kungiyoyin kasa da kasa domin tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da anfani da sabbin fasahohi wajen kula da albarkatun tekunta da hanyoyin ruwa.
