Gwamnatin Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta kara kaimi wajen inganta lafiyar mata ta hanyar kaddamar da amfani da na’urar High-Intensity Focused Ultrasound (HIFU) a Asibitin Wuse District, domin magance cutar fibroid da wasu matsalolin mahaifa ba tare da tiyata ba.
Masana sun bayyana cewa wannan fasaha za ta kawo sauyi mai girma wajen kula da cutar fibroid da kuma wasu matsalolin da ke haddasa cututtukan sankarar mahaifa ga mata.
An gabatar da na’urar ne a lokacin Makon Lafiyar Haihuwa na Renewed Hope 2026, inda cibiyar Nordica Fertility Centre ta bayar da gudummawar na’urar ga asibitin.
Sakatariyar Lafiya da Muhalli ta FCT, Dakta Adedolapo Fasawe, ta ce cutar fibroid na daga cikin matsalolin da suka fi addabar mata, inda take haddasa yawan zubar jini, ciwo, rashin haihuwa da kuma matsaloli yayin daukar ciki.
Ta ce saboda karfafa mata gwiwar neman magani, gwamnatin FCT za ta bai wa mata 100 na farko da suka cancanta damar samun wannan magani kyauta.
Shugaban Nordica Fertility Centre, Dakta Abayomi Ajayi, ya bayyana cewa sama da mata 940 sun riga sun amfana da wannan hanyar magani, yana mai cewa suna fatan nan gaba kadan za su kai mata 1,000 da aka yi wa magani cikin nasara.
Masana sun yi bayanin cewa HIFU na amfani da igiyoyin sauti masu karfi da ake mayarwa zuwa zafi domin lalata ƙwayoyin cutar ba tare da bude jiki ko amfani da maganin barci ba.
Sun kara da cewa wannan hanya na rage lokacin kwanciya a asibiti da kuma saurin murmurewa bayan jinya, tare da ba mata damar ci gaba da fatan haihuwa idan sun dace da irin maganin.
Masu ruwa da tsaki sun yi kira da a kara zuba jari a sabbin fasahohin kula da lafiyar mata, horas da ma’aikatan lafiya da kuma fadakar da jama’a domin mata su rika zuwa gwaji da neman magani da wuri.
Haka kuma sun shawarci mata masu fama da yawan jinin al’ada, ciwon mara, kumburin ciki ko matsalolin haihuwa da su gaggauta zuwa asibiti domin samun cikakken bincike maimakon dogaro da magungunan da ba a tabbatar da ingancinsu ba. :::
