Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama wani da ake zargi da zama babban dillalin miyagun kwayoyi bayan sun kai samame wani sansanin masu laifi a yankin Ikot Ebom Itam da ke karamar hukumar Itu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Timfon John, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Ofonime Etim yayin wani samame da jami’ai suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
A cewarsa, jami’an sun kai farmaki wani wuri da ake zargin mafakar masu safarar miyagun kwayoyi ne, masu karɓar kayan sata da kuma masu lalata kayayyakin gwamnati.
Binciken da aka gudanar a wurin ya kai ga gano miyagun kwayoyi da ake zargin tabar wiwi ce, takardun nannade taba, gatari, adduna, wayoyin lantarki da aka lalata, zanen rufi, tagogin aluminium, kayan abinci da na sha, giyar haram da kuma wasu kayan lantarki da ake zargin sata aka yi su.
Mazauna yankin sun yabawa rundunar ‘yan sanda kan wannan nasara, suna mai cewa ayyukan wanda ake zargin da abokan huldarsa sun dade suna barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’umma.
Haka kuma shugaban kauyen ya tabbatar da cewa daya daga cikin kayan da aka kwato, famfon ruwa na rijiyar zauren kauyen Ikot Ebom Itam ne wanda aka sace a baya.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya amsa laifin satar famfon ruwan yayin binciken farko da jami’ai suka gudanar.
‘Yan sanda sun ce bincike na ci gaba domin gano masu sauran kayan da aka kwato tare da kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a lamarin.
