Makarantar Horar da Sojojin Ƙasa ta Najeriya (NASI) ta yaye ɗaliban kwasa-kwasan Advance Airborne Course 31, Basic Rigger Course 48, Basic Airborne Course 61 da kuma NDA Cadets Basic Airborne Course 10 bayan sun kammala adadin tsalle-tsallen soja daga jirgin sama da ake buƙata domin zama ƙwararrun paratroopers.
An gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a Jaji Drop Zone ranar 4 ga Yuni, 2026, inda aka nuna ƙwarewa, shirin yaƙi da kuma kwarewar sojoji a fagen aikin sama.
Da yake jawabi a wajen bikin, Kwamandan Rundunar Infantry Corps, Manjo Janar Godwin Michael Mutkut, ya buƙaci sabbin sojojin da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen ƙarfafa ayyukan tsaro da kare martabar ƙasar Najeriya.
Ya jaddada muhimmancin jajircewa, ƙwarewa da sadaukar da kai wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A cewar sanarwar da Kyaftin Shamsudeen Umar, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na NASI ya sanya wa hannu, Mutkut ya kuma bukaci waɗanda aka yaye da su ci gaba da nuna ladabi, jarumtaka da ƙwarewa a duk inda za a tura su aiki.
A nasa jawabin, Kwamandan NASI, Manjo Janar Frank Sunday Etim, ya bayyana cewa ɗaliban sun samu horo mai tsauri wanda ya haɗa da motsa jiki, dabarun aikin sama da kuma shirye-shiryen ƙarfafa tunani kafin su cancanci sanya alamar airborne wings.
Ya ce sun nuna ƙwazo, juriya da kwarewa a lokacin horon, yana mai tunatar da su cewa aikin sama na buƙatar cikakken lura da daki-daki domin kauce wa haɗurra.
Haka kuma, makarantar ta yaye ɗaliban kwas ɗin Armoured Personnel Carrier (APC) Driving and Maintenance Section Commanders Course 40, inda aka umarce su da su yi amfani da ƙwarewar da suka samu wajen tafiyar da motocin yaƙi da kuma koyar da sauran jami’ai a wuraren aikinsu.
Bikin ya ƙare da tsalle-tsallen kammala horo, sanya alamar airborne wings ga waɗanda suka cancanta, rabon kyaututtukan yabo da kuma ɗaukar hoton tunawa.
